Yaushe malaman jami’a za su daina yajin aiki a Nijeriya?

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Wani al’amari da ke ci wa ’yan Nijeriya tuwo a ƙwarya, musamman iyaye da ɗaliban manyan makarantu shi ne yajin aikin ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU, wanda ya qi ci ya ƙi cinyewa. Duk kuwa da ƙoƙarin da gwamnati ta ce tana yi, na biyan wasu buƙatun ƙungiyar da ɗaukar matakai kan wasu matsalolin da ƙungiyar malaman take ƙorafi a kansu. 

Yawan yaje yajen aiki da ƙungiyar malamai ta ASUU take tafiya kusan a kowacce shekara, ya fara ƙure iyayen yara da ƙungiyoyin ɗalibai, waɗanda ke zargin sakacin gwamnati da nuna halin ko-in-kula da ƙungiyar ASUU ke yi da al’amarin karatun su, suna masu cewa shugabannin ƙasar nan da masu faɗa a ji ba sa nuna damuwa kan abubuwan da ke faruwa ne, saboda ’ya’yansu na karatu ne a jami’o’in ƙasashen waje, inda ba a san da wani abu wai shi yajin aiki ba. 

A farkon wannan mako mai ƙarewa, Gamayyar Ƙungiyoyin Ɗaliban Nijeriya ta NANS, ta gudanar da wata zanga-zangar lumana a dukkan faɗin ƙasar nan har da Babban Birnin Tarayya Abuja, domin bayyana rashin jin daɗinsu da kwan gaba kwan bayan da ake yi kan wannan batu na yajin aikin malaman jami’o’i, waɗanda a daidai lokacin aka ce suna kan cigaba da tattaunawa da a tsakanin ɓangarorin gwamnati da na malamai. 

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban ƙungiyar ɗalibai ta NANS, Sunday Ashefon ya bayyana halin ƙuncin da ɗaliban jami’o’i a Nijeriya ke ciki sakamakon wannan yajin aiki da ASUU ke yawan tafiya, inda kuma ya buƙaci a gaggauta kawo ƙarshen yajin aikin gargaɗi na wata guda da ƙungiyar malaman ke ciki, da kuma shigar da wakilcin ɗalibai cikin tattaunawar da ake yi tsakanin gwamnati da ƙungiyar ASUU.

Buƙatar da Ministan ilimi Malam Adamu Adamu ya amince da ita, sai dai kuma ya nuna rashin jin daɗin wasu zarge-zarge da aka ce ƙungiyar ɗaliban ta yi a gaban sa na cewa, da gangan ake wasa da makomar karatun ’ya’yan talakawa a Nijeriya, tun da an kasa kawo ƙarshen wannan yajin aiki, mai yiwuwa saboda akasari yaran su a makarantun ƙasashen waje suke karatu, zargin da aka ce ya vata wa Ministan rai, har ya fice ya bar ɗaliban, saboda ɓacin ran cin fuskar da ɗaliban suka nuna masa, duk da faɗi tashin da gwamnati ke yi na shawo kan lamarin. 

Wani ɓangare na jawabin shugaban qungiyar ɗaliban da aka ce shi ya fi harzuƙa Ministan shi ne wurin da shugaban ƙungiyar ta NANS ke cewa, “Mai Alfarma Minista, a kwanakin nan ne ta zaurukan sada zumunta muka ga hoton ka kana bukin murna da kammala karatun ɗanka a wata jami’a ta ƙasashen waje. Mu iyayen mu ba su da halin da za su kai mu karatu wata ƙasar waje, amma muna son mu ci moriyar kuɗaɗen makaranta da muke biya.”

Shi kuwa Minista Adamu Adamu, an rawaito yana ce musu, su je su binciki malaman su, kan dalilin da ya sa suke yajin aikin. Amma ya amince da buƙatar su ta neman a shigar da wakilcin ƙungiyar NANS cikin tattaunawar da ake yi. 

Babu shakka za a iya cewa, tura ta kusa kai wa bango ga ‘yan Nijeriya, sakamakon wannan matsala ta yajin aikin da irin waɗannan ƙungiyoyi ke tafiya lokaci zuwa lokaci, kusan ba tare da wata doguwar tazara ba.

Daga a ce ƙungiyar malamai ta ASUU, sai ka ji an ce ƙungiyar ma’aikatan jami’o’i da ba sa koyarwa, ko kuma ƙungiyar malaman kwalejojin kimiyya da fasaha ta ASUP da ma kwalejojin manyan makarantu masu zurfafa bincike da sauran su. Har ma wani lokaci da ƙungiyar haɗin gwiwar ’yan kasuwa da masu masana’antu ta TUC. 

A cikin makon nan ne ma, shi shugaban ƙungiyar ta TUC, Kwamred Quadiri Olaleye ya yi barazanar cewa, ƙungiyar za ta bi sahun ƙungiyar ASUU wajen shiga yajin aikin ƙasa baki ɗaya, matuqar ba a samar da matsaya kan wannan tataɓurza da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa ba, domin mara wa ƙungiyar malamai da ta ɗalibai baya. 

Wani abin takaici da ɗaure kai shi ne, waɗannan ƙungiyoyi ba sa tashi da batun wannan yajin aikin da suka ce shi kaɗai ne makamin da suke da shi, sai sun ga wani muhimmin al’amari ya taso wa ƙasa, wanda gwamnati ke ƙoƙari a kansa, kamar dai batun shirye shiryen zaɓe na ƙasa ko kuma yayin tattauna batun gyaran kundin tsarin mulki, ko bitar kasafin kuɗin ƙasa. Ba tare da la’akari da a wanne matakin karatun ɗalibai suke ba, a tsakiyar jarabawa, ko ana daf da fara jarabawa ko kuma dai wani yanayi mai matuƙar muhimmanci ga ɗalibai.

Wannan al’amari yana matuƙar ci wa ɗalibai tuwo a ƙwarya ba kaɗan ba, ganin yadda karatun nasu ke komawa baya, wani lokaci kuma dalilin yajin aikin wasu ɗalibai kan jefa rayuwar su munanan halaye, irin su shaye-shaye, sace-sace, fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma karuwanci ga ɗalibai mata. 

A cewar ƙungiyar ASUU, wannan yajin aikin ya zama musu dole ne, domin da shi ne kaɗai suke da damar amfani da shi wajen matsa wa gwamnati lamba ta saurari koke koken su, waɗanda akasari ba na ƙashin kansu ba ne, ya shafi cigaban harkokin ilimi da inganta tafiyar da jami’o’i, abin da suka ce kwalliya tana biyan kuɗin sabulu, domin an samu sauye-sauye da dama da suka ce gwamnati ta yi su ne, saboda takurawar ƙungiyar malamai. 

A wani jawabi da ya yi wa manema labarai, shugaban ƙungiyar ASUU na ƙasa, Emmanuel Osodeke ya bayyana cewa, tsawon shekara tara kenan gwamnati na yi musu alƙawura, amma ba ta iya cika wa. Da zarar an janye yajin aiki, sai a sake komawa gidan jiya. Don haka sun gaji da gafara sa ba su ga ƙaho ba. 

Ƙungiyar ta bugi ƙirjin cewa, malaman jami’o’i na matuƙar ƙoƙari wajen ganin ɗalibai ba su samu matsala a karatun su ba, domin kuwa, wasu malaman har jingine batun hutun aikin su suke yi, don ganin sun cike guraben da aka samu sakamakon yajin aikin da ake yi. 

Gwamnatin Tarayya a nata ɓangaren, ta koka da yadda buƙatun ƙungiyar malamai yake ja wa gwamnati kashe maqudan kuɗaɗe, wanda yanzu haka akwai yarjejeniyar da gwamnati da ASUU suka sanya wa hannu da za ta ci wa gwamnati Naira Biliyan 200 duk shekara har tsawon shekara biyar, domin farfaɗo da tsarin tafiyar da jami’o’i. Sannan ga batun taƙaddamar sabon tsarin biyan albashin malamai da sabon tsarin IPPIS na gwamnati da wanda su kansu malaman jami’o’in suka ɓullo da shi na UTAS, wanda har yanzu ba a warware ba. 

Lallai akwai buƙatar ɓangarorin nan biyu su samar da fahimtar juna a tsakanin su, matuƙar duk fafutukar nan ilimi ake so ya inganta, kuma makomar matasan ƙasar nan ake so a gyara. Kada gwamnati ta yi sake abin ya fara wuce makaɗi da rawa, ya kai matakin da wasu harkokin tafiyar da ƙasa za su tsaya, matsalolin tsaro su ƙara lalacewa. 

Da fatan iyayen qasa da sauran masu faɗa a ji za su sa baki a shawo kan wannan matsala, waɗanda abin ya shafa su ma za su yi aiki da hankali wajen duba wasu hanyoyi na maslaha da za a riƙa isar da koke da warware damuwa ba tare da ya shafi karatun ɗalibai a jami’o’i ba. 

Da fatan su ma ƙungiyoyin ɗalibai za su yi kyakkyawan tsari na gabatar da ƙorafin su ba tare da sun bari wasu baragurbin ‘yan siyasa sun yi amfani da su wajen kawo ruɗani a ƙasa, domin cimma wata manufa ta son zuciyarsu ba.