‘Ya’yana mata duk Hausawa suka aura, kuma ba wacce ta taɓa yaji – Sarkin Ebran Kano da Jigawa

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Alhaji Ohinoyi Abdulmalik Atta, Sarkin Ebran Kano da Jigawa, dattijo mai shekara 81 a duniya, ya bayyana cewa ƙabilyar Ebra ƙabila ce mai cike da zaman lafiya da wadatar zuci da kwanciyar hankali a duk inda suka samu kansu, don haka suna da yawa a tsakanin jihar Kano da Jigawa dama sauran jihohin Arewacin Nijeriya baki ɗaya, inda ya ce yana farin ciki da godiya ga Allah na yadda al’ummar ƙabilar Ebra ta kasance masu zaman lafiya da jama’a a ko’ina kuma ‘ya’yansu mata masu biyayya ne ga aure ko da wadata ‘ya’yanmu suka auri mutum to indan ma ba wadatar ba za su canja biyayya a garesu ba kuma muna da kyakkyawar fahimta da Hausawa da ma sauran ƙabilun Nijeriya, domin yanzu haka cikin ‘ya’yana sama da 30 da Allah ya ba ni a duniya akwai ‘ya’ya mata 9 da dukkaninsu Hausawa su ka aura kuma babu wacce ta taɓa yaji a cikin su ko wani saɓani da za a ji tsakanin ta da mai gidanta da za a ji har akai ruwa rana kuma haka abin ya ke a mafiya yawa na ‘ya’yan mu ‘yan ƙabilar Ebra kamar yadda Ohinoyi Abdulmalik Attaya ya bayyana a hirarsa da manema labarai a fadar sa ta Kano da Jigawa.

Haka kuma ya ƙara da cewa tun lokacin da ƙabilar Ebra ta zo Kano a shekaru masu ɗimbin yawa tana da kyakkyawar alaƙa da masarautar Kano da al’ummar kuma babu wani abu a tsakanin Ebra da al’ummar Kano musamman shugabannin al’umma da su kansu al’ummar sai alkairi don haka ne kowanne abu ne na daɗi ko akasin sa ya faru a masarautar Ebra ta can ko ta nan zakaga alumma da shugabanin suna tururwa wajen taya su murna ko akasin murna wannan abin farin ciki ne ga alumma ebra na Kano da Jigawa da suka kai duban gomomi a wannan shiyya da ma Arewa baki ɗaya.

A ƙarshe ya ce da naɗa shi wannan sarautar ta haura shekara 20 kuma ana zaune lafiya da kyakkyawar fahimta don haka ya yi kira ga ɗaukacin sauran ƙabilu da ma wanda ba ƙabila ba  sun yi koyi da alumma Kano wajen karɓar baki da ƙarrama su da rashin nuna banbancin harshe da sauransu kuma mu Ebra mutane ne masu neman na kanmu da taimakon juna dama sauran a duk inda muka samu kanmu wajen kishin al’umma ƙasa da ma Nijeriya baki ɗaya.

By ukarofi