Gidauniyar Bafarawa ta duba tare da bayar da magani ga marasa lafiya 400 a Sakkwato ta Arewa

Spread the love

Daga AISHA ASAS

A cigaba da taɓo kowane ɓangare na rayuwar al’ummar Sakkwato da kuɗin da tsohon gwmanan Jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayar, ƙarƙashin shirin Mayar da Alheri da Alheri, kwamitin gudanarwa na gidauniyar tare da haɗin gwiwa da ƙaramin kwamiti na ƙaramar Hukumar Sokoto ta Arewa, sun gudanar da gangamin duba marasa lafiya a ƙarƙashin jagorancin Uban Kasar Sabon Birni, da kuma Garka.

Taron wanda aka gudanar a harabar ofishin Uban ƙasa biyu da ƙaramar hukumar ta ke da, wanda ke cikin ƙaramar hukumar, ya samu halartar ƙwararrun likitoci har guda shida, da kuma malaman jinya, tare da masu awon jini.

Tun daga farko, shugaban babban kwamiti, Malam Lawal Maidoki, wanda ya samu wakilcin Malam Kabiru Binji, ya bayyana yadda shirin zai kasance, da kuma irin tanadin da aka yi wa bayin Allah da suke ɗauke da lalura ta ciwo, kuma ba su da abin da za su kai kansu asibiti, inda ya bayyana cewa, za su ga likita a ɓangaren abinda yake damunsu, kafin su karɓi magani kyauta, daidai da abinda likita ya rubuta.

Wani abin ƙarin birgewa ga shirin kuwa shi ne, yadda kwamitin ya yi tanadi na musamman ga marasa lafiya da matsalarsu ke buƙatar fiye da abinda za a iya ba su a wurin, wato kamar ciwon da ke buƙatar tiyata.

Malam Binji ya bayyana cewa, za su karɓi lamabar marar lafiyar, su saka a takardarshi, inda za a yi kiransa zuwa asibiti don ba shi kulawar da yake buƙata.

Da yake jawabi a madadin ƙaramin kwamiti na ƙaramar Hukumar Sokoto ta Arewa, mataimakin shugaban kwamitin Alhaji Kabiru Dodo, ya soma da godiya ga shugaban tafiyar ta gabaɗaya, wato  Lawal Maidoki, Sadaukin Sakkwato, inda ya yi masa godiya kan namijin ƙoƙarin da yake yi na ganin an kwatanta adalci a duk wani tallafi da za a bayar ba tare da duba ɓangaranci ba ko siyasa.

Alhaji Kabiru ya ci gaba da bayyana irin ayyukan alkhairai da gidauniyar ta Attahiru Bafarawa ke yi da kuma waɗanda take kan hanyar aiwatarwa, inda ya sanar da rabon tallafin abinci buhu ɗari da kuma miliyan ɗaya da ta yi ga kowacce ƙaramar hukuma cikin ƙanannan hukumomi 23 da ke akwai a Jihar Sokoto, wato dai buhu 2,300 kenan da kuma miliyan ashirin da uku ne suka zagaye jihar ta Sokoto.

Baya ga tallafin tiyata ga marasa lafiya da ke kwance asibiti ba halin da za a yi masu tiyatar da likitoci suka buƙata a yi don samun lafiyarsu. Wannan kuwa shiri ne da shi Sadaukin Sakkwato ya jagoranta har kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Har ila yau dai, gidauniyar ta kai masu lalurar taɓin hankali biyu daga kowacce ƙaramar hukuma asibiti, inda za ta kula da su har zuwa ranar da warakar Allah za ta riske su.

Ba a iya nan ba, gidauniyar ta shirya gyaran maƙabartu, gina rijiyoyi da kuma gyaran bohol, da share hawayen kowacce ƙaramar hukuma na daga wani aiki da ta jima tana so a yi mata.

A ɓangaren waɗanda suka amfana da wannan tallafin, sun yaba wa irin tsarin da aka yi, na wanda ya zo farko a fara da shi, inda hakan ya hana ba wa wani ɓangare fifiko, sannan sun yaba wa ƙoƙarin gidauniyar na samar masu da magunguna masu inganci.

ɗaga daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin, ya shaiɗawa wakiliyar Blueprint Manhaja cewa, magungunan da aka ba shi a nan suna da matuƙar tsada, dalilin da ya sa ya ce haka kuwa, ya je asibiti a kwanaki, likita ya rubuta masa su, saidai da ya je ɗakin shan magani, ya kasa siya saboda yawan kuɗin da aka kira masa.

Yananyin tsari da ƙwarewar da ma’aikatan suka nuna a wurin bai zama abin ban mamaki ba, kasancewar shugaban tafiyar ƙwararre kuma gogagge a wannan fanin. Don haka idan muka ce Allah Ya saka wa tsohon gwamna Alhaji Attahiru ɗalhatu Bafarawa da mafi alkhairi kan wannan bajimin ƙoƙari da ya yi, za mu kuma yi kwatankwacin wannan addu’ar ga Sadaukin Sakkwato kan jajircewar da ya yi na ganin wannan alherin ya isa ga waɗanda aka bayar don su kamar da gwamnan ya buƙata.

By ukarofi