Yuguda ya bayyana Tinubu a matsayin mai amana

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda ya bayyana dalilansa na goyon bayan shugabancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da ya danganta da riƙon amanarsa, musamman tsakaninsa da Shugaba Muhammadu Buhari.

“Kamar yadda muka sani, Allah ya yi ikonSa, Tinubu shi ne sanadi da ya sanya masoyinmu Muhammadu Buhari ya zama shugaban ƙasar Nijeriya. Inda bai ba shi goyon baya ba, bani tsammani zai kasance shugaba, in bacin wata ƙaddara ta Ubangiji,” inji Yuguda.

Yuguda, wanda yake yi wa manema labarai jawabi a garin Bauchi, ya kuma bayyana cewar, “Tinubu ya riƙe mu da amana, dalili kenan da ya sanya muka riqe shi amana, kamar yadda muka nuna masa a lokacin zaɓen shugaban qasa da aka yi a kwanakin baya.

“Na biyu kuma shi ne ya cancanta, la’akari da ire-iren ayyukan cigaba da ya aiwatar a Jihar Legas lokacin da yake riƙe da kujerar Gwamna. Ya gina birnin Legas, ta kuma ɗaukaka tamkar manyan biranen Turai, ko Makka da Madina da mutanen mu suka fi yawan zuwa.”

Yuguda ya ƙara da cewar, “Yau kusan kowace irin masana’anta da jama’a suka sani, akwai ta a Legas. Yawancin kayayyakin abinci da muke ci, muke sha, hatta tufafi da muke sanyawa duk a Legas ake yin su. Allah shi ne ya yi ikon haka, Tinubu shi ne sanadi.”

Tsohon gwamnan na Bauchi ya ce Allah ya bai wa Tinubu basira na sarrafa abubuwa, musamman sarrafa dukiya, haɗi da ƙwamatsa mutane bisa fahimtar juna da aiwatar da muhimman abubuwa domin amfanin jama’a.

Malam Isa Yuguda don haka sai ya yaba wa jama’ar Jihar Bauchi bisa yadda suka bai wa Tinubu cikakken goyon baya a lokacin zaɓen shugaban ƙasa da na majalisun ƙasa da suka gabata, yana mai cewar, “Idan ka duba yawan ƙuri’u da Tinubu ya samu a jihar Bauchi, ya fi na ire-iren waɗanda gwamnonin jihohin APC suka samu.”