Zannan Kwankwasiyya ya raba tallafin injinan bada wuta ga makarantun islamiyya a Jihar Kano

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Jigo a tafiyar Kwankwasiyya a qaramar hukumar Nasarawa, Alhaji Abubakar Yahuza Gama, Zannan Kwankwasiyya ya tallafa wa wata ɗaliba Fatima Aminu da ta yi nasarar zama ta ɗaya a musabaƙar karatun Ƙur’ani da kayan ɗaki tare da bai wa makarantun Islamiyya 48 injinan bada wutar lantarki don haskaka makarantun, ƙarƙashin ƙungiyar haɗin kan makarantun Islamiyya.

A yayin taron da aka gudanar a ɗakin taro na Mento a ranar Alhamis, Zannan na Kwankwasiyya ya kuma bada kyautar firji guda biyar ga ɗaliban makarantun Islamiyya da suka yi nasara a musabaƙa na Sira da sauran fannoni na addini.

Da yake ƙarin haske ga ‘yan jarida kan maƙasudin taron, Alhaji Abubakar Yahuza Gama ya ce  taron na cika alƙawarin da ya yi wa ɗaliban ne a madadin Dokta Rabiu Musa Kwankwaso da ɗan takarar Gwamnan Jihar Kano na cewa za a yi wa ɗalibai da makarantunda suka nuna hazaƙa wannan tagomashi musamman ma ga wacce ta yi na ɗaya a musabaƙar Ƙur’ani.

Alhaji Abubakar Yahuza Gama ya ce dama irin wannan tagomashi suna yi na tallafawa cigaban makarantun Islamiyya, amma saboda sun shiga harkokin siyasa ya sa ake bibiyarsu ake sanin abinda ake.

Ya ce da yardar Allah irin wannan tallafi zai cigaba fiye da haka a dukkan faɗin jihar nan, don haka suna kira ga al’ummar jihar Kano su baiwa takarar Abba Kabir Yusuf goyon baya don kaiwa ga nasarar zama Gwamnan jihar Kano da yardar Allah don bunƙasa makarantun Islamiyya.

Yace dama can tun tsawon lokaci yana hidima don cigaban makarantun Islamiyya tun yana malami da yake zuwa ya kai ɗalibai Maulidi har yake zuwa a matsayin babban baƙo.

Zannan na Kwankwasiyya ya ce kowa ya san ƙungiyar haɗa kan makarantun Islamiyya a ƙaramar hukumar Nasarawa tun suna yara suka ga tana hidima har suma suka taso suka gada suka shigo, ba a taɓa samun wata shekara da aka ce ba a gudanar da Maulidin Manzon Allah ba a yankin ƙarƙashin ƙungiyar.

Abubakar Yahuza Gama ya ce da a ce babu wannan irin ƙungiyar da sai za a zo ma watan Maulidin ya wuce ba a ma sani ba. Don haka ma ƙungiyar ta tashi daga matakin ƙaramar hukumar Nasarawa ta koma ta Jihar Kano baki ɗaya.

Ya ce don haka ma  ya nemi alfarma wajen ɗan takarar Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da yardar Allah in ya zama Gwamnan Jihar Kano ƙungiyar ta shiga ta zama ɗaya daga hukumomin gwamnati kamar yadda ake da hukumar Sharia, Zakkah da Hubusi, amma babu wata da take tafi da raya soyayyar ma’aiki, in aka kai ga nasara da yardar Allah za a tabbatar da da wannan a matsayin hukuma, inji shi.

Ya yi nuni da cewa wannan kayan ɗaki da aka bayar alƙawari ne na ɗan takarar Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da ya yi wa ɗaliba da ta yi na ɗaya a musabaƙa shine ya bayar a madadinsa da kuma firji da aka ba ɗalibai guda biyar maza da mata. 

Ya ce an kuma samar da injinan wutar lantarki da ƙungiyar haɗakar makarantun Islamiyya  ta bada sunayensu a wurare daban-daban ɓangarori daban-daban don cigaba da bunƙasar makarantun.

Zannan na Kwankwasiyya ya yi kira ga ‘yan makarantun Islamiyya da suka isa kaɗa ƙuri’a su bai wa ɗan takarar Gwamna Kano na NNPP Injiniya Abba Kabir Yusuf goyon baya yara kuma da ba su isa zave ba su yi ta addu’a don Allah ya ba su nasara a zaɓen Gwamna mai zuwa.

Taron dai ya samu halartar wasu jiga-jigai da masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar NNPP a ƙaramar hukumar Nasarawa da jihar ta Kano.