
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanannen mawaƙin Nijeriya, David Adeleke da aka fi sani da Davido, ya yi iƙirarin cewa gwamnatin Amurka ta ba shi amsa kan kokawa da ya yi game da zaɓen da ke tafe na gwamnan jihar Osun.
Davido ya yi wannan tsokaci ne a sahfinsa na kafar X yayin da al’amuran siyasa a ihar suka yi kamari gabanin zaɓen, wanda za a gudanar a ranar Asabar.
Kawun mawaƙin, Gwamna Ademola Adeleke na jihar, na neman a sake zaɓar sa a karo na biyu a kujerar gwamnan jihar a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar AP, wato Accord Party.
Davido dai ya kasance mai tsokaci akan lamuran zaɓen tun bayan kaɗa gangarsa a makonnin da suka gabata, inda yake nuna damuwa kan yadda da za a gudanar da zaɓen tare da tabbatar da gaskiya da adalci akan haka.
A cewarsa, akwai buƙatar ƙasashen waje su sanya ido game da al’amuran da ake gudanarwa gabani, yayi da kuma bayan zaɓen.
Iƙirarin nasa na kwanan na zuwa ne yayin da harkokin siyasa ke cigaba da gudana a jihar, inda magoya bayan ‘yan takara daban-daban suke faɗaɗa yaƙin neman zaɓe yayin tunkarar ranar zaɓen ta 15 ga Agusta.
Da fari dai, Davidon ya yi magiya ga Shugaba Donald Trump da wasu jiga-jigan siyasar duniya da su kirayi hukumomin Nijeriya kan su kare masu zaɓe da tabbatar da an gudanar da sahihin zaɓe ba tare da rikici, wulaƙanci ko hargitsa al’amura ba.
Bayan sa’o’i da wannan kira ne sai mawaƙin ya koma shafin nasa na X ya yi iƙirarin cewa ya samu amsa daga gwamnatin ta Amurka. Saidai bai bayar da ba’asi akan amsar da ya samu ba daga wakilanta.
Ga abin da ya rubuta ta harshen Turanci: “Dem don reach out ooooo. DEY PLAY! U think the rest of the world is undemocratic like Una! Una go see something.”
