Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Tinubu ya tafi hutu ƙetare

Daga BASHIR ISAH

Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Nijeriya mai jiran gado, Bola Tinubu, ya tafi hutu Paris a ƙasar Fransa inda daga nan zai tafi Saudiyya domin aikin Umarah.

Bayanin haka ya fito ne ta bakin mai magana da yawun Tinubu, Tunde Rahman, cikin wata sanarwar da ya fitar ranar Laraba.

“Bayan kammala harkokin kamfe da zaɓe, zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Asíwájú Bola Tinubu, ya keta hazo domin hutawa da kuma tsara yadda shirin karɓar mulki zai kasance a ranar 29 ga Mayun 2023,” in ji Rahman.

A cewarsa, Tinubu ya bar Babban Filin Jirgin Saman Murtala Mohammed da ke Ikeja zuwa Turai ne ranar Talata da daddare.

Ya ƙara da cewa, “Zaɓaɓɓen Shugaban ya yi tafiya domin ya huta a Paris da London bayan kammala harkokin zaɓe, kuma daga can zai tafi Umarah da Azumin Ramadan a Saudiyya.”