Za a yi fim na farko wanda mata zalla ne suka shirya a Kannywood

Daga AISHA ASAS

Da yamma, a cikin cunkoso irin na Jihar Kano, Aisha Abubakar Usman, ke tsaye a gefen titi, ta na jiran lokaci mafi cancanta ta tsallake titin Zoo Road mai yawan kaiwa da komowa.

Wannan layi na Zoo Road ƙwarai ya cancanci a kira shi da layin Kannywwod, kasancewar yana ɗauke da mafi yawa daga cikin masu harkar fim a garin na Kano.

Kalmar Kannywwod suna ne da aka sanya wa masana’antar da ke arewacin Nijeriya, wato Hausawa.

Kuma kalmar ta samo sunanta ne daga sunan Jihar Kano, inda ya zama mazauni ko in ce cibiyar mafi yawa daga cikin masu harkar fim.

Isar Aisha ke da wuya ta samu wurin zama cike da jin daɗin isa muhallin da ta yi muradin zuwa.

Jarumar dai ta dawo ne daga lokeshon inda ta haɗu da takwarorinta mata masu shirin fara wani namijin aiki da zai zama irinsa na farko a tarihin finafinai, kuma sun ɓata wunin ne wurin duba wurare, a ƙoƙarinsu na shirin fara aikin.

Aisha Abubakar tare da mata 29 da mafi yawansu ‘yan’uwanta ne jarumai da kuma wasu ɓangarori na harkar ta finafinai, sai kuma ƙwararrun ‘yan jarida, ɗalibai da kuma mambobin wasu daga cikin ƙungiyoyin mata da aka zaɓa domin shayar da su ilimin harkar fim tun daga farko har zuwa gaɓar da zata samar da hoto mai magana a akwatunan talabijin, wato fim.

Tunanin waɗannan jajirtattun mata bai tsaya iya kutsawa don a dama da su a masana’antar Kannywwod ba, har da kawar da kallo da banbancin da ake nuna wa mata a sana’ar dalilin da ke kawo tasgaro ga cigabansu, wanda ke hana mata irinsu kai wa ga nasarar cin kasuwa a kasuwar finafinai ta Nijeriya, wato Nollywood, wadda a yanzu ta ƙara armashi albarkacin zuwan Netflix, Amazon da kuma Showmax.

A wannan zama da jarumar ta yi tare da Binta Usman Abdullahi, Ummusalma Isa, Maryam Abubakar Ruffy da kuma Fatima Danjuma, zama ne na tattaunawa kan wuraren da za a gudanar da aikin.

Aisha ta kwashe tsayin shekaru biyar a masana’antar finafinai ta Kannywood a matsayin jaruma da ke taka rawa a finafinai.

Ta fito cikin finafinai da dama, tun daga masu dogon zango har zuwa shirye-shiryen talabijin da sauransu.

Sai dai kamar sauran da suka kwankwaɗi wannan ilimi na harkar fim, wannan ne karon farko da za ta yi aiki a bayan kamara, wato dai sarrafa kayan aikin.

“Wannan ne karon farko da zan samu kaina a aiki tare da sanin yadda ake sarrafa kamara, lasifika da sauran kayan aikin,” inji ta.

Waɗannan jajirtattun mata sun haɗu ne don kafa tarihi a masana’antar ta Kannywood ta hanyar zama na farko a tarihin masana’antar da suka fitar da fim ɗin mata zalla, wato fim ɗin da mata zalla suka ƙyanƙyashe shi ba tare da aiki da namiji ko ɗaya ba.

Ita ma Binta Usman kamar dai Aisha ce, tsayin shekaru biyar da ta yi a masana’antar ba ta taɓa sanin yadda ake amfani da kayan aikin ba sai ta sanadiyyar wannan horo da suka samu, wanda a yanzu zata taka rawa a aikin samar da shirin fim ɗin da suke ƙuduri.

“Ban san komai dangane da aikin saitin zane (set design) kafin wannan horo da aka ba mu. Yanzu na san komai da ya jiɓince shi, kuma da wannan shirin fim da muke yunƙuri, na san zan iya yin kafaɗa da kadaɗa da ‘yan’uwanmu maza da ke cikin wannan harkar,” inji Binta.

Ita kuwa Ummusalma Isa ta fito ne daga wata duniyar ta daman da ta su, kasancewar ta ɗaliba mai karatun lauya, ta samu kanta a cikin su ta sanadiyyar ƙungiyar da ta ke ciki da ta turo ta, inda ta ce, ta ji daɗin hakan.

Ɗalibar wadda a yanzu ta ke taka matsayin mataimakiyar furodusa a aikin ta ce, “ni ma’abuciya son finafinai ce, kuma wannan horon ya ba ni damar sanin yadda ake haɗa shi, hakan kuwa ba ƙaramin daɗi ya yi min ba.”

Cike da soyayyar abinda ta koya, Ummusalma ta bayyana tunani na biyu da take da shi na zavar abinda ta ke karatu a matsayin abinda za ta yi wa raywarta ƙawa da shi. Ta ƙara da cewa, “Ban sani ba ko zan iya haɗa su biyun ba, amma dai dole zan zavi ɗaya a cikin biyun. (aikin fim ko lauya)”.

Maryam Abubakar Ruffy, wadda zata haɗa taura biyu a lokaci ɗaya ta tauna a aikin, wato fitowa jaruma da injiniyan sauti, ta bayyana matsayin wannan horo a wurin ta, inda ta ke cewa, “wannan horas wa buɗe ido ne game da harkokin masana’antar fim, inda mata ba su cika samun dama ba. Mun samu abinda zai sa mu ma a dama da mu a ɓangaren.”

The Girds Nation and the Women’s International Film Festival Nigeria ne suka bayar da wannan horon bitar, yayin da Ofishin Jakadancin Faransa suka taimaka, inda a ƙarshe, kowacce ɗaya daga cikin mata 30 da aka zaɓa don ba su wannan horon zata gabatar da gajeren fim na tsayin mitina 30, wanda za a haska shi a ranar bikin finafinai don nuna baiwa da kuma ilimin da suka samu.

Ita kuma furodusan fim ɗin Halima Ben Umar, wadda sunanta ke cikin jerin sunayen 30, ta bayyana wannan aiki na su a matsayin bada gudunmawa ga al’umma kuma hanyar ba wa mata ‘yan Arewa damar bajekolin fasahar su a duniyar finafinai.

Kazalika hanya ce ta kawo canji kan yadda ake keɓence mata a wasu ɓangarori na masana’antar Kannywwod.

Halima wadda saura ke kira da mama, kasancewar ita ce mafi shekaru a cikin su, ta kasance tana jagorantar ƙungiya mai zaman kanta, wadda ake kira da ‘Women in Media Initiative’ kuma ofishinta ne hedkwatar wannan namijin aiki da suke shirin farawa. Duk da cewa wannan ne karo na farko da zata yi aiki irin wannan, Halima cike ta ke da ƙwarin gwiwa.

Bilkisu Yusuf Ali, ɗaya daga cikin waɗanda suka jima suna hidimtawa masana’antar Kannywwod, kuma ɗaya daga cikin mata 30 da suka samu wannan horon, ta bayyana muhimmancin horon da yadda ya ba su damar yin aikin cikin sauƙi.

“Na samu tsayin shekaru goma a masana’antar Kannywwod a matsayin marubuciyar finafinai, kuma akwai littattafai da dama da na rubuta. Don haka, wannan horo da muka samu ba abinda muke buƙata sai mayar da hankali tare da dagewa wurin samar da ingantaccen labari wanda zai dace da irin ma’aunin tunanin da muka yi. Kuma alhamdu lillah, mun yi nasarar yin hakan,” a cewarta.