Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A yayin take shirin gudanar da bikin cika shekaru 25 da kafuwa, ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (AFC) ta ce za ta ci gaba da jajircewa wajen kare kai da kuma inganta muradu da ƙimar Arewa.
Shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar, Alhaji Dalhatu Wazirin Dutse, ya tabbatar da haka a lokacin da ya jagoranci sauran mambobin ƙungiyar ta ACF a ziyarar ban girma da suka kai wa Gwamna Nasir Idris a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi a ranar Talata.
Alhaji Dalhatu ya sanar da mai masaukinsu cewa an kafa dandalin ne a shekara ta 2000, wanda yanzu ya cika shekaru 25, wanda za a yi bikin daga 20 zuwa 22 a Kaduna.
“Da farko dai, an kafa ƙungiyar ACF ne domin ta kare muradun Arewa a fannin tattalin arziki da zamantakewa, har ma da siyasa, amma mun kasance ba jam’iyya ba.
“Muna da sha’awar siyasa musamman abubuwan da suka shafi Arewa.
Dalhatu ya ce, “ACF ta samu ci gaba sosai wajen cika aikinta, ta samu nasarori wajen kare rayuwar Arewacin Nijeriya.”
Ya kuma yaba wa Gwamna Nasir Idris bisa salon jagoranci da tsare-tsaren sa na ci gaba da kuma tsare-tsare masu dacewa da jama’a na raya jihar Kebbi.
Shugaban ya ƙara da cewa, “Mai girma gwamna, muna godiya gare ka da gwamnatinka, ACF na goyon bayanka kuma tana goyon tafiyarka a al’amuran jihar.”
Shugaban hukumar ta ACF, Mamman Mike Osman, SAN, ya shawarci gwamnan da ya yi taka-tsan-tsan kan ayyukan ‘yan fashi da makami, irin su Lakurawa, da suke tashe-tashen hankula da aikata laifuka ga ‘yan ƙasa da ba su ji ba ba su gani ba.
A martaninsa Gwamna Nasir Idris ya ce, Kebbi za ta yi duk mai yiwuwa don tallafa wa ACF ta kowace hanya da ta dace.
