Za mu dakatar da rufe layukan sadarwa Talata mai zuwa – Matawalle

Daga Sanusi Muhammad, Gusau

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya yi alƙawarin buɗe hanyoyin sadarwa a sauran ƙananan hukumomi 13 na jihar a ranar Talata mai zuwa.

Matawalle ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan rantsar da sabbin zaɓaɓɓun shugabannin jam’iyyar APC na jihar a ranar Asabar.

A cewarsa, rahotannin da gwamnatin sa ta samu sun nuna cewa an rage matsalar rashin tsaro zuwa mafi ƙaranci.

“Mun samu rahoton leƙen asiri cewa an kawar da barazanar ‘yan bindiga fiye da kimai don haka za mu sake buɗe hanyoyin sadarwa tsakanin Litinin ko Talata”, inji Matawalle.

Ya kuma yi kira ga mutanen jihar da su kwantar da hankulansu tare da marawa duk wasu tsare-tsare da manufofi na gwamnati don ci gaban jihar.

MANHAJA ta rawaito cewa Hukumar Sadarwa ta Ƙasa tare da haɗin guiwar gwamnatin jihar Zamfara a watan Satumban da ya gabata sun rufe hanyoyin sadarwa a faɗin ƙananan hukumomin jihar 14 domin rashin tsaro sakamakon ayyukan ‘yan bindiga da suka addabi jihar.