‘Yar Jamhuriyar Nijar ta farko da ta yi nasara a gasar Hikayata

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

An haifi Nana Aicha Hamissou Abdoulaye a ranar 27 ga watan Yuli, 1994 a unguwar Sabon Gari da ke garin Maraɗi. Ta fara karatun boko a shekarar 2000, ta yi digirinta na farko a fannin muhalli. Yanzu haka kuma tana cigaba da karatun digiri na biyu a fannin rabe-raben rayuwa da Muhalli a jami’ar Abubakar Ibrahim da ke Maraɗi a Ƙasar Nijar.

Nana Aicha Hamissou Abdoulaue ta samu ilimin addini mai zurfi, inda ta sauke Alƙur’ani Maigirma a watan Disamba, 2013. Mahaifin Nana Aicha ta rasa mahaifinta a shekarun da suka gabata, inda yanzu haka take zaune da mahaifiyar ta, kuma ba ta da aure.

Gwarzuwar gasar wadda ta zo mataki na biyu, kuma ta kasance ‘yar Ƙasar Nijar ta farko da ta tava samun nasara a gasar Hikayata ta BBC Hausa, ta ce ta fara yin rubutu a watan Afrilun shekarar 2019, yayin da yawan karance-karance ta ya sa ta tsinci kanta a duniyar Marubuta.

Nana Aicha Hamissou Abdoulaye ta ce ta fi son karanta labaran da suka jiɓanci tausayi, wanda zai sanya ta ta dinga sharɓa kuka har da hawaye. Bugu da ƙari ta ce tana son littafan soyayya mai cike da ƙalabale da sarƙaƙiya.

Gwarzuwar wadda ta nuna cewa ƙasar Nijar ita ma ba kanwar lasa ba ne a fannin adabin Haisa, kuma ta haska irin ƙoƙarin ‘yan ƙasar a wannan gasa ta 2021, ta ce tana ƙarƙashin ƙungiyar Marubuta Hausa ta ‘Kainuwa Writers Association’ mai hedikwata a garin Kano.

A wajen bikin karrama gwarazan gasar, Nana Aicha Hamissou Abdoulaye ta samu kyautar dala 1000 da kambun karramawa tare da takardar shaida.

Da yawan mahalarta taron dai sun nuna farin cikin su da yadda Nana Aicha Hamissou ta fito gaban taron don amsar kambun karramawarta, inda ta yi sujjada, ta ɗora goshinta a ƙasa don nuna godiyarta ga Allah bisa nasarar da ta samu.

Haka zalika ta kuma yi kira ga sauran marubuta mata ‘yan uwanta da su cire shakku ko fargaba a duk lokacin da za su shiga gasar ta Hikayata a shakara mai zuwa. Ta bayyana cewa duk abin da ake gwadawa akai-akai wata rana za a kai ga yin nasara.

Daga ƙarshe Nana Aicha ta kuma yi godiya da kafar BBC da ta ba mata wannan dama ta nuna fasahar su a fagen rubutu, ta ce hakan zai taimaka wajen ƙarfafa wa matan guiwa ta ɓangaren rubuce-rubuce da maida hankali a kansa, duba da yadda wasu suka ɗauki rubutun Hausa ko Hausar a matsayin abu mara muhimmanci, injita.

Wata ‘yar ƙasar Nijar dai ba ta tava zuwa matakin gwarazan gasar Hikayata ba tun da kafar BBC Hausa ta vullo da wannan gasa shekaru kusan huɗu sai a wannan karon, inda mutane da yawa suke ganin wani mataki ne na ɗaukar gasar da muhimmanci fiye da yadda aka soma da farko.

A wannan shekarar an samu marubuta mata daga ƙasashen Ghana, Kamaru, Sudan da Nijar da suka aike da labaran su. Haka kuma marubuta’yan Nijeriya waɗanda ke zama a ƙasar Saudiyya da Italiya da sauran wuraren su ma ba a bar su a baya ba wajen aikewa da labaran su.