Za mu samar da sababbin hanyoyin magance barazanar tsaro – Janar Musa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Babban Hafsan Tsaro na Ƙasa (CDS), Manjo Janar Christopher Gwabin Musa, a ranar Alhamis, ya yi kira da a samar da sababbin hanyoyin magance matsalolin tsaro da ke kunno kai a faɗin ƙasar nan.

Musa ya yi wannan kiran ne a Abuja, yayin da yake bayyana ra’ayinsa na shugabancin rundunar sojin Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da shi da kansa ya sanya wa hannu, Musa ta ce, ɗimbin ƙalubalen tsaro da ke cigaba da taɓarɓarewa a ƙasar, Nijeriya na kira da a ɗauki ƙarin matakai domin daƙile su.

Bisa la’akari da haka, Musa ya bayyana cewa, ya himmatu wajen tabbatar da ingantaccen yanauin tsaro don kare rayuka da dukiyoyi don ayyukan zamantakewa da tattalin arziki su cigaba.

Janar Musa ya bayyana cewa, babban fa’idar shugabancinsa zai kasance “Don Rayar da Ƙwararrun Sojoji na Nijeriya, Haɗin Kai kuma da Ƙarafafa Ayyukan Kundin Tsarin Mulki a Haɗin gwiwa”.

Saboda haka, Musa ya ƙara da cewa, manufar shugabancinsa za ta dogara ne akan ginshiƙai guda uku waɗanda suka haɗa da kasancewa mai son jama’a, ba da fifiko ga jin daɗin sojoji da haɗin gwiwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *