Za mu sasanta da Sarkin Kano, don mutum ne mai dattaku – Air Peace

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban kamfanin jirgin sama na Air Peace, Allen Onyema ya bayyana cewa hukumomin kamfanin za su ziyarci Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, nan ba da daɗewa ba don tattaunawa kan abinda ya faru.

A makon da ya gabata ne aka ɗan samu rashin jituwa tsakanin Fadar Sarkin Kano da Kamfanin na Air Peace a yayin dawowar sarkin zuwa Kano da ga tafiyar da ya yi zuwa wasu ƙasashe na Afirka.

Sai dai kuma Onyeama ya bayyana cewa ba zai bari wannan rashin fahimta ya tada ƙura ba saboda ya san Sarkin Kano mutum ne mai son zaman lafiya.

Ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da shugabannin kamfanin jaridar Daily Independent.

“Ban san wannan abun ya tada hazo haka ba, kuma ba na so kamfanin Air Peace ya zama musababbin tada hatsaniya a ƙasar nan.

“Na kasance mutum mai son zaman lafiya. Tun lokacin da na ke da ƙananan shekaru. Don haka zan yi abun da ya dace domin kashe wannan wutar.

“Saboda haka ba zan bari a yi amfani da ni wajen raba ƙasar nan ba. Na daɗe da sanin Sarkin Kano tun yana Ciroma, lokacin da mahaifinsa ke da rai.

“Za mu haɗu wata rana, na san ba mutum ne mai son rigima ba kuma ina da tabbacin zai so ya haɗu da ni kuma ni ma ina son haɗuwar da shi ” inji Onyeama.

A cewar Onyema, babu wata matsalar da wannan saɓanin zai haifar.