Yadda hada-hadar cinikin ’yan wasa ke kasancewa

Daga WAKILINMU

Ƙungiyar Paris Saint-Germain ta shirya tsaf, don bai wa ɗan wasan ƙungiyar mai shekara 23 Kylian Mbappe sabon kwantiragi kan albashi mai ɗimbin yawa na Yuro 799,000 a duk mako, domin ya zauna, inda ita kuma Real Madrid ta ce, tana son sayen ɗan wasan na Faransa.

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti, mai shekara 62, ya bayar da mamaki bayan ya shiga cikin jerin waɗanda ake sa ran za a zaɓa, domin zama kocin Manchester United na gaba.

Bayern Munich da Tottenham da Arsenal suna son sayen ɗan wasan bayan Middlesbrough xan ƙasar Ingila mai shekara 21, Djed Spencer, wanda a halin yanzu ya tafi aro Nottingham Forest.

Tsohon ɗan wasan tsakiyar Everton da Colombia, James Rodriguez, mai shekara 30, ya sa ƙungiyarsa ta Everton ta zama cikin shiri bayan ya nuna alamun yiwuwar komawarsa daga Qatar.

Barcelona na sa ran shawo kan ’yan wasan bayan Chelsea da Denmark, wato Andreas Christensen, mai shekara 25 da kuma Cesar Azpilicueta na ƙasar Sifaniya, domin su koma ƙungiyar kyauta a ƙarshen wannan kakar.