Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Shugaban Jam’iyyar PDP na jihar Kano Hon. Yusuf Ado Kibiya ya yi kira ga al’mma musamman ‘yan jam’iyyar da cewa ya kamata su shiga taitayinsu domin yanzu magana ta jihar Kano ake ya wuce maganar jam’iyya, duk mai son Kano in da gaske yake yi ya sake tunani ya zo a yi tsari da zai taimaki al’umma.
Ya bayyana hakan ne a taron rantsar da shugabannin jam’iyyar PDP na ƙananan hukumomi 15 na Kano ta tsakiya, inda ya ce duk mai tunanin kansa ko shi ya isa ko babu wanda ya iya sai shi to ba Kano yake so ba, kowa ya sani yau na cikin matsala jihar Kano ita ce fitilar Nijeriya, amma yau ita ce koma baya.
Ya ce tsarin su na jam’iyyar PDP a ƙarƙashin jagorancin Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau za su duba mene ne ke damun Kano me ye matsalar ta. Jam’iyyar PDP in dai Kano kake so sun bada dama kowa ya shigo cikinta ya zo ya bada gudunmuwa da zai taimaki al’umma.
Hon. Yusuf Ado Kibiya ya nuna takaicinsa bisa abinda ke faruwa a Kano a halin yanzu domin da a baya duk inda mutumin Kano ya je abin sha’awa ne, amma yanzu ba haka ba ne. Jam’iyyar su ta PDP ƙarƙahin tsarin da suka fito da shi za su assasa matakai da za a kai ga nasara a sami shugabanci na gari su da aka zaɓe su burinsu fitar da shugabanci da zai taimaki al’ummar jihar Kano.
Ya yi nuni da cewa idan Kano ta samu Arewa ta samu, idan Arewa ta samu Nijeriya ta samu, abin takaici da yake faruwa a Kano mutane sun yi zaɓe a makance yau ga shi sune suka fi kowa asara, in ka je kasuwa ‘yan kasuwa za su gaya maka, haka aikin gwamnati ma’aika za su gaya maka.
Hon. Yusuf Ado Kibiya ya ce ‘yan siyasa sune koma baya kullum, abinda ake cewa ka tura mota ta tashi ta bule ka da ƙura ake musu sai tsiraru sun shaƙe siyasa akan buƙatarsu. A shirye suke su bada jagoranci na babu sani ba sabo domin inganta jam’iyyar.
Shi ma a jawabinsa Malam Ibrahim Shekarau ɗaya da jagororirin jam’iyyar PDP a jiyar Kano ya ce dokokin zaɓe na kowace jam’iyya bana PDP kaɗai ba, ta tanadi matakai na zaɓe na yin maslaha da na jefa ƙuri’a wannan kuma duk sunansa zaɓe.
Don haka yana tunatar da masu shure-shure su koma su karanta kundin tsarin mulkin jam’iyya ya kuma ƙalubalanci duk wani mai ja da zaɓuɓɓuka da suka yi su kawo musu shaidar inda suka yi ɗauki ɗora ba yabon kai ba, tun daga mazaɓa har aka ƙare babu inda Sardaunan Kano ya ce ga wane nan koda a mazaɓarsa ta Giginyu amma don tabbatar da yi wa kowa adalci ba wani waje da su jagorori suka aika cewa lallai lallai a zaɓi wani,idan ma wani ya ce wanin su ya yi ƙarya yake.
Shi ma a nasa ɓangaren mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na Kano ta tsakiya, Alhaji Kabiru Bello ɗandago ya shawarci sabbin shugabannin jam’iyyar na PDP na ƙananan hukumomi 15 na Kano ta tsakiya da aka rantsar su mayar da jam’iyya hannun mutane domin sune jam’iyya.
ɗandago ya ce duk wanda yake da sha’awar jam’iyyar PDP a tuntuɓe shi a yi shawara dashi inda za a kai jam’iyyar tudun mun tsira, shine cin zaɓen 2027 kuma wannan nasara ba za ta samu ba sai sun yi haƙuri da juna da mutumtawa da haɗa kai da fito da yan takara ingantattu na kwarai sannan asa su a gaba sannan su ci zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.