Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
‘Yan majalisar wakilai 15 cikin 18 da aka zaɓa a Jam’iyyar NNPP a jihar Kano sun amince da tsige ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Dala, Ali Madaki, a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar.
A cikin wata takarda da Manhaja ta gani a ranar Litinin, ‘yan majalisar da ba su amince da cire Madakin Gini ɗin ba su ne Alhassan Rurum na Rano/Kibiya/Bunkure da Abdullahi Sani na ƙaraye/Rogo.
A cikin wata wasiƙa da aka aika zuwa ga shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, tare da haɗin gwiwar shugaban jam’iyyar NNPP da sakataren jam’iyyar NNPP Ajuji Ahmed da Dipo Olayoku, shugabannin jam’iyyar sun gabatar da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Dawakin Tofa/Tofa/Rimingado, Tijjani Jobe, a matsayin wanda zai maye gurbin Madakin Gini.
“Mun rubuta wannan wasiƙa ne domin miƙa sunan babban ɗan jam’iyyarmu, Hon. Tijani Abdulkadi Jobe domin maye gurbin Hon. Aliyu Sani Madaki a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar,” wani sashe na wasiƙar ya ce.
Duk da cewa ba a bayar da dalilin tsige Madaki ba, jaridar Manhaja ta ruwaito cewa hakan ba ya rasa nasaba da cewa Madaki a kwanakin baya ya fice daga tafiyar Kwankwasiyya, kuma ya yi mubaya’a ga wanda ya kafa jam’iyyar, Boniface Aniebonam.