Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Edo, Sanata Monday Okpebolo, ya amince da kafa kwamitin tantance kadarorin jihar mai mutane 14, domin binciken gwamnatin tsohon gwamnan jihar Godwin Obaseki.
Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan, Fred Itua ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Ya ce kwamitin wanda za a ƙaddamar da shi a ranar Talata 26 ga watan Nuwamba, 2024, a gidan gwamnati da ke birnin Benin, Dr Ernest Afolabi Umakhihe ne zai jagoranta.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “A ci gaba da shirin da gwamnan ya yi na ɗora jihar kan turbar ci gaba da kuma shugabanci na gaskiya, kafa kwamitin tantance kadarorin jihar ya zama wajibi.
“Duk da kiraye-kirayen da aka yi na a samar da cikakkun bayanai na kadarorin gwamnatin da ta shuɗe, amma gwamnatin Godwin Obaseki ta bayar da bayanai kaɗan ne kawai.
“A daidai da alƙawarin da gwamnan ya yi a yaƙin neman zaɓe na tabbatar da gaskiya, riƙon amana a harkokin gudanar da mulki, an kafa kwamitin da ya ƙunshi maza da mata a jihar Edo.”
Yayin da Anslem Ojezua zai zama mataimakin shugaba, Frank Edebor zai yi aiki a matsayin sakatare.
Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Kassim Afegbua, Patrick Ikhariale, Taiwo Akerele, Patrick Idiake, da Rasaƙ Bello-Osagie. Karin membobin sun haɗa da Fredrick Unopah, Abdallah Eugenia, Patrick Obahiagbon, Kenny Okojie, Lyndsey Tes-Sorae, da Abass Braimoh.
Okpebholo a jawabinsa na farko a ranar 12 ga watan Nuwamba ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta binciki fitar da ‘yan majalisa 14 daga majalisar dokokin jihar a shekarar 2019.
A ranar Juma’a, gwamnan ya ba da umarnin gudanar da bincike kan ɗaukar ma’aikatan jihar ƙarƙashin Obaseki tsakanin watan Mayu zuwa Nuwamba 2024.
Idan za a tuna, Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya shawarci Okpebolo a kan binciken gwamnatin Obaseki mai barin gado.
Ya ba da shawarar ne a lokacin da Okpebolo ya kai ziyarar ban girma a kwamitin ayyuka na jam’iyyar (NWC), a ranar 31 ga Oktoba.
Ganduje ya roƙi Okpebolo da ya mayar da hankali wajen ɗora mulki na gari idan ya hau mulki.
“An kiyaye manufofin dimokuraɗiyya, an aiwatar da zaɓen, kuma muna kan cin nasara, bai kamata ku mai da hankali kan gwamnatin da ta gabata ba. A tunkari gaba, kada ku waiwaya baya, kuma kada ku ɓata lokacinku don yaƙar mutumin da kuka gaje shi, babu buƙata. Gwamnati mai ci gaba ba ta da lokacin yin hakan.
“Ku mai da hankali kan takardar da kuka samar da himma, ku bi ta har zuwa wasiƙar tare da ci gaban zamantakewa da tattalin arziƙin jama’a, ku gina gadoji. Kafa kyakykyawar alaƙa da masu ruwa da tsaki, a yi tunani gaba sannan ka zama gwamna mai aiki,” Ganduje ya shawarci.