Zambar haraji: Kotu ta ɗaure Ancelotti shekara ɗaya a gidan yari

Spread the love

Wata kotu a Sifaniya ta yanke wa tsohon kocin Real Madrid Carlo Ancelotti hukuncin shekara ɗaya a gidan yari saboda kauce wa biyan haraji game da kuɗaɗen da ya samu na haƙƙin mallakar hotonsa.

Kotun ta yi hukunci ne kan lamarin da ya faru a 2014 lokacin da yake horar da Real Madrid, inji wani rahoton da aka fitar a ranar Laraba.

Ancelotti, wanda ya horar da Real Madrid daga 2013 zuwa 2015 da kuma 2021 zuwa 2025, an taɓa wanke shi a irin wannan zargin a 2015.

Ya koma Landan a watan Mayun 2015 bayan da Real Madrid ta kore shi.

Sai dai a ƙarƙashin dokar Sifaniya, duk wani hukunci da ke kasa da shekara biyu idan bai shafi tashin hankali ba, yana da wuya a bukaci wanda ake tuhuma ba tare da an taɓa yanke masa hukunci a baya ba ya yi zaman gidan yari.

Mai shekara 66 ɗin da ya horar da Bayern Munich da Chelsea, shi ne na baya-bayan nan da hukumomin Sifaniya suka bincika da yanke hukunci kan zambar biyan haraji.

By ukarofi