Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludo, ya bayyana cewa mafi yawan laifukan da ake aikatawa a yankin Kudu maso Gabas Inyamurai ne ke aikata su.
Ya ce, saɓanin yadda ake yaɗawa, kashi 99.9 cikin 100 na masu laifin da aka kama kan ayyukan ta’addanci da sauran miyagun ɗabi’u ‘yan ƙabilar Ibo ne.
Mista Soludo ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga ’yan asalin Anambra a Amurka a wajen taron da aka gudanar a Maryland.
Ya ce: “Waɗanda ake kira masu ’yantarwa da ke ɓoye a cikin dazuka ’yan gida ne masu aikata miyagun laifuka suna cin gajiyar kuɗin jini. Suna fitowa da iƙirarin cewa su ne ke kare ku daga makiyaya Fulani.
“Suna zaune a daji na tsawon watanni, amma babu wanda ya taɓa tambaya yadda waɗannan masu kiran kansu ’yan ’yantarwa ke rayuwa a daji. Dole ne su ci abinci, wa ke biya musu buƙatun su, ashe ba su da buƙatu?”
“A cikin shekaru uku da watanni uku na mulki, kashi 99.99 cikin 100 na masu garkuwa da mutane da sauran masu laifi da muka kama ‘yan ƙabilar Ibo ne. Mu daina yaudara. Ibo ne ke yin garkuwa da mutane da kisan ’yan uwansu Ibo, ba Fulani ba.”
