Daga HABU ƊAN SARKI a Jos
A ranar Juma’a, gaban Babbar Kotun Jiha ta 10, an gurfanar da mutane 20 da ake zargi da kai hari da kisan mutane 13 da ba su ji ba, ba su gani ba, a unguwar Mangun da ke ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato, sun musanta laifukan da ake tuhumar su da su guda huɗu.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Filato shi ya gabatar da ƙarar a ƙarƙashin lamba PLD/J115/2025, inda ake tuhumar Rabiu Haruna, Julius Abaris, Clement Machel, Gideon Istifanus, Bamkat Dan’doka, Dauda Ezekiel, Lawrence Samaila, Mantu Daniel, Gabriel Sunday, Steven Luka, Joel Danladi, Plankat Ayuba, Nanfan Habiba, Frances Augustine, Andy Danladi, Gungret Appolos, Bamshak Letak, Titus Bakwet, Balmun Helon da Chutse Salvation, da sauran mutum shida.
Ana zargin su ne da laifukan haɗa baki wajen aikata laifi, amfani da makamai masu haɗari, amfani da fetur da wuta, kisan kai, haddasa ɓarna mai tsanani da kuma kashewa da kona mutane 13 a ranar 20 ga Yuni, 2025. Waɗannan laifuka sun ci karo da sashi na 59 na dokar manyan laifuka, da sashi na 220, 313 da 189 na dokar Jihar Filato ta 2017.
“A ranar 20 ga Yuni, 2025, a Mangun da ke ƙaramar hukumar Mangu, cikin ikon wannan kotu, kun yi tattaki da makamai masu haɗari kamar bindigogi, adda, man fetur da sauransu, ba tare da wani dalili ba, kun kai hari kun ƙona mota mai ɗaukar mutane 18, sannan kuka kashe”.
“Aminu Samaila, Abdullahi Abdulwahab, Isa Abubakar, Malam Sani, Ibrahim Sani, Ramatu Danladi, Adamu Sani, Ma’awe Habibu, Alhaji Mukhtari Ahmad, Sani Abdullahi, Hamisu Danladi da Baba Sani Hamisu, wanda hakan ya zama kisan kai mai laifi bisa sashi na 189 na dokar laifukan Jihar Filato ta 2017,” kamar yadda aka gabatar da tuhume-tuhumen.
Bayan sun musanta laifin, Lauyan masu ƙara, Samuel I. Ikutanwa, ya buƙaci kotu da ta ɗage ƙarar domin gudanar da tsarin shari’a.
Ya kuma buƙaci a ba da umarnin tsare waɗanda ake tuhuma a cibiyar gyaran hali ta Jos.
Lauyan masu kare kansu, Garba Paul SAN, bai yi gardama kan buƙatar tsare waɗanda ake tuhuma ba, ya ce hakan daidai ne bayan sun amsa tuhuma, a fara bibiyar shari’ar.
Sai dai ya gabatar da buƙatar beli, wanda Lauyan masu ƙara ya ki amincewa da shi, yana mai cewa doka ta ba su kwana bakwai su mayar da martani, amma kotu na shirin tafiya hutun bazara wanda hakan ba zai yiwu ba.
Mai shari’a Boniface Ngyong ya yanke hukunci cewa ba za a saurari buƙatar belin ba, bisa la’akari da batun hutun kotu da Lauyan gwamnati ya bayyana.
Ya shawarci lauyan waɗanda ake tuhuma da ya kai buƙatar belin gaban alƙalin kotu lokacin hutu.
Mai shari’a Ngyong ya ɗage sauraron ƙarar zuwa 13 ga watan Oktoba, 2025.
“Kuma waɗanda ake tuhuma su cigaba da kasancewa a cibiyar gyaran hali ta Jos,” in ji hukuncin.
