Zamfara: Ƙungiyar Marafa ta nemi ɗanfulani ya yi murabus daga shugabancin APC

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Alhaji Surajo Garba Maikatako, Shugaban ƙungiyar goyon bayan Jam’iyyar APC ɓangaren Sanata Kabiru Garba Marafa a Jihar Zamfara ya yi kira ga shugaban jam’iyyar APC na jihar, Hon Tukur ɗanfulani da ya yi murabus daga muƙaminsa domin samun zaman lafiya da cigaban jam’iyyar APC a jihar.

Surajo Maikatako ya yi wannan kiran ne a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau ranar Alhamis. 

Maikatako ya ƙalubalanci Hon ɗanfulani da mayar da Sanata Marafa saniyar ware tare da nuna wariya ga Sanata Marafa da magoya bayansa a jihar.

A cewarsa, za a iya magance rikicin jam’iyyar APC a jihar Zamfara ne kawai idan Tukur ɗanfulani ya ajiye mukaminsa na shugaban jam’iyyar a jihar, yana mai cewa bai cancanta da shugabancin jam’iyyar ta APC ba a jihar.

Ya ƙalubalanci cewa Hon. Tukur ɗanfulani ya karkata ga waɗanda suke goyon bayansa da bashi kuɗaɗe, yana mai jaddada cewa son ransa ya jawo wa jam’iyyar matsaloli da dama a jihar Zamfara.

Hon Surajo Maikatako ya bayyana shugabancin Tukur ɗanfulani a jihar Zamfara a matsayin wanda ya gaza, inda ya bayyana cewa ya cika kwaɗayi. 

“Na dage cewa Tukur ɗanfulani ya yi murabus nan take, saboda shugabancinsa gazawa ne kuma yana haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar a jihar”. Maikatako ya bayyana 

A cewarsa, Sanata Kabiru Garba Marafa da jiga-jigan magoya bayansa ‘yan jam’iyyar APC,  yana ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar APC a jihar.

Hon. Surajo Maikatako ya yi kira ga magoya bayan Sanata Kabiru Garba Marafa da su kwantar da hankalinsu da haɗin kai da kuma bin doka da oda domin ci gaban jam’iyyar APC a jihar Zamfara.

By ukarofi