Zamfara: An kulle gidan mai da na burodi bisa Zargin alaƙa da ‘yan bindiga

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kwamitin bibiya na Jihar Zamfara ya bi bi umarnin Gwamna Bello Matawalle kan matsalar rashin tsaro, ya bada umarnin rufe gidan mai da gidan burodi a ƙananan hukumomin Gusau da Tsafe a jihar.

Shugaban kwamitin, Abubakar Dauran ne ya bayar da wannan umarni jim kaɗan bayan jami’an tsaro sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi da bayar da burodi da fetur ga ‘yan bindiga.

Dauran, kuma mai bai wa Matawalle shawara kan harkokin tsaro, ya ce za a rufe gidan man da ke garin Tsafe a ƙaramar hukumar Tsafe, bisa zargin sayar da man fetur ga ‘yan ta’adda, yayin da za a rufe gidan burodi da ke Gusau, wanda ke bada burodi ga ‘yan bindiga.

“Duk gidan mai da gidan burodi za a rufe nan take,” in ji shi.

A cewarsa, an kama waɗanda ake zargin ne bayan an sanya musu ido, daga bisani kuma jami’an tsaro da ke da alaƙa da kwamitin bibiya suka bi su.

“An samu wasu daga cikin waɗanda ake zargin suna amfani da jarkunan galan da tankunan janareta wajen siyan man fetur daga gidajen mai tare da ba wa ‘yan bindiga a maɓoyarsu.

“An kama su ne ɗauke da man fetur zuwa ƙauyen Yanware na ƙaramar hukumar Tsafe, yayin da aka kama waɗanda ake zargin suna sayar da burodi ba bisa ƙa’ida ba, suna amfani da babura wajen kai burodin ga wasu da ba a san ko su waye ba, waɗanda ake zargin ‘yan bindiga ne.”

Ya koka da cewa duk da ƙoƙarin da gwamnan yake yi na samar da dawwamammen mafita ga matsalolin tsaro da ke addabar jihar,” wasu marasa kishin ƙasa ne ke yi wa yunƙurin zagon qasa. gwamnati za ta aiwatar da umarnin zartarwa ga wasiƙar, yana mai gargaɗin cewa waɗanda suka karya doka, idan aka kama su, za su fuskanci fushin doka.

Shugaban kwamatin ya yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da bai wa gwamnati da jami’an tsaro goyon baya da bayar da sahihan bayanai kan ‘yan bindiga da masu haɗaka da su domin ɗaukar matakin da ya dace. Ya yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare kan masu taimaka wa ‘yan bindigar da garkuwa da mutane a jihar.