Kannywood: Mafari da makoma

Daga AL’MUSTAPHA ADAM MUHAMMAD

Wasan kwaikwayo wani al’amari ne mai daɗɗaɗen tarihi a rayuwar ɗan Adam. Ya samo asali ne shekaru aru-aru da suka wuce a daulolin Girkawa da Rumawa tun ɗaruruwan shekarun da suka shuɗe. Tun a wancan lakacin akan yi amfani da wasan kwaikwayo ne don nishaɗantarwa da zaburar da rundunonin sojojinsu da suka yi nasara a yaƙe-yaƙen su a wancan zamani. Haka zalika akan yi wasannin kwaikwayo don faranta wa masu mulki rai su samu cikakken muwalati da nishaɗi. A irin waɗannan lokuta ne makaɗa, masu iya bada hikayoyi, maraya da mutanen fadla masu barkwanci kan sheƙe ayar su gaban manyan hafsoshin soja don ɗebe kewa.

To ana haka ana haka dai har irin wannan ɗabi’a ta rinƙa bazuwa zuwa sauran nahiyoyin duniya na daulolin Larabawa, Farisa, da sauran su.

Daga nan sai harkar wasan kwaikwayo ta bunƙasa ta zama ruwan dare yadda har masu hannu da shuni kan yi jinga da irin waɗannan masu wasan kwaikwayo domin biyan wasu buƙatun su na nishaɗi da shaƙatawa. Nan da nan sai wasan kwaikwayo ya zama sana’a wadda ta bazu ko ina da ina a duniya. Wata sa’a ma sabili da banbancin harshe sai a shiga alamta abubuwa da hannu wato dai kwaikwayon mu’amala ta zamantakewa.

Haka dai al’amura suka riƙa gudana har kimanin ɗaruruwan shekaru da suka wuce yayin da masana’antu suka fara kankama a yanmacin Turai. Daga nan fa sai wasan kwaikwayo ya bazu aka riqa yinsa a duk wani wuri da jama’a kan taru don nishaɗi.

A nan Ƙasar Hausa, ana iya cewa wasan kwaikwayo ya daɗe ainun tamkar yadda al’adar gargajiya ta faro. Daga nan kuma har al’amura suka ƙara inganta bayan da aka kafa gidan Radio Television Kaduna a zamanin Marigayi Firimiyan Jihar Arewa, Alhaji Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato.

Tsakanin shekarar 1963 zuwa wajen 1965 aka fara wasan kwaikwayo na talabijin mai suna ‘Kukan Kurciya’. A cikin shirin ne akan tsara wasa don nusar da al’umma managartar hanyoyin mu’amala da kyakkyawar zamantakewa. A lokacin ne irin su Alhaji Bawa Garba wato Shugaban Kamfanonin ABG Communications da su Harira Kachia da su Ƙasimu Yero, lokacin yana xan saurayi, suka fara fito da wasan kwaikwayo fili. Wannan yana daga cikin hoɓasar farko-farko da takai ga samuwar masana’atar shirya fina-finan Hausa wacce aka fi sani da Kannywood. 

Kannywood, haɗakar kalmomi biyu ne aka haɗe su zuwa ɗaya, Kano da kuma Wood. Ana ganin an kwaikwayo hakan ne daga Hollywood da Bollywood kamar yadda Sunusi Shehu Daneji wanda ya samar da ita kalmar Kannywood a shekarar 1999 ya faɗa. Tun daga loakacin ake kiran masana’atar da suna Kannywood. 

Kamar yadda yake a fahimtar magabata, fim wani ɓangare ne daga kafar sadarwa ta lantarki wadda take samar da gani da ji da motsi, domin amfanin mutane masu yawa, kuma yare ne da kowane mutum yake iya fahimtarsa a duniya. Fim tantagaryar kimiyya da fasaha ce, kuma rayuwar ɗan’adam ce ake nunawa. Fim yana ɗauke da tarihi da ɗabi’un jama’a da muhallinsu da abincinsu da kuma suturarsu, musamman bisa harshensa da tsarinsa na rayuwa da hanyoyin tunaninsa da kuma falsafar rayuwar mutanen da ake yin fim ɗin don su. Har ila yau, fim hanya ce ta sanarwa da ilmintarwa da jan hankali da nishaɗantarwa da faɗakarwa da yaɗa manufa da tallatawa. A dunƙule kafa ce daga cikin kafafen yaɗa labarai, sannan kuma hanya ce ta kasuwanci da samar da aikin yi ga ɗimbin al’ummar da babu wata masana’anta da ta samar a ƙasar nan kamar ta. 

Ko da yanzu da wasu ke kallon masana’antar na shure-shuren mutuwa amma hakan bai hana tururuwar ɗinbin matasa maza da mata daga ko’ina a faɗin ƙasar da wajen ta shigowa Kano don shiga masa’anatar ta shirya fina-finai ba. Hakan ke ƙara alamta matuƙar tasirin ta ga al’umma. Ba iya matasa kaɗai ba, har ma da dattijai na kwarara cikinta, lamarin da manazarta ke alaƙanta hakan da katutun da ɗaurin gwarman da talauci ya yi wa mutane.

Wasu kuma ana su hangen, kwaranyowar masu shiga harkar ta fina-finan na Hausa ba ya rasa nasaba da buƙatar son a sani da neman suna ko shahara ta yarda wasu ke amfani da hakan wajen samun muwalati, ko dai daga masoya ko tallace-tallace daga kamfanoni. Ƙila ma shi ne dalilan da yasa duk da mutuwar da wasu ke ganin masana’antar ta yi hakan bai sa gwiwar wasu matasa sarewa ba suka bazama neman mafita gudun kar duniyar ta daina tunawa da su, ya sa suka fara bubbuɗe ‘channel-channel’ na ‘YouTube’ lamarin da wasu ke kallon hakan a matsayin ci gaba, wasu suke kallo a matsayin akasin hakan. Kamar yadda wani Darakta Mansoor Sadiq, ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki a masana’antar yake cewa,  “Tururuwar buɗe ‘channel-channel’ na ‘Youtube’ ga ‘yan masana`antar, idan ka duba wani ɓangaren koma baya ne, amma kuma idan ka duba ɓangare ɗaya kuma ci gaba ne, saboda duk wanda ruwa ya ci shi ko takobi ka ba shi kama wa zai yi.”

Da na tamabaye shi ko me yake tunanin ya haifar da durƙushewar masana`antar shirya fina-finai ta Kannywood har a ka koma ‘YouTube’? Daraktan sai ya ka da baki ya ce,
“Abubuwan da suka durƙusar da harkar shirya fina-finai a Kannywood suna da yawa, amma abin da suka fi kowanne ba su wuce uku ba. Ka ga akwai rashin sanin darajar harkar fim ɗin. Babu yadda za ayi mutum a matsayin sa na ‘producer’ ya kashe naira miliyan biyar ya yi fim, amma ya ji ƙyashin cire dubu arba’in da zai sayi ‘hard drive’ guda biyu ko uku da zai yi ‘backup’ ɗin aikinsa. Ko ka ga mutum ya yi aiki a matsayin sa na darakta amma anyi aiki har an gama ‘editing’ amma bai sani ba duk da mafi yawan lokuta mamallaka aikin ne ba sa sanar da shi. Ko kuma ka ga mutum ya yi aiki a matsayin sa na jarumi amma ya kasa bayar da gudummawa wajen tallata aikin. Ko kuma ka ga wasu jarumai musamman ma matan mafiya yawan su sunan suka fi buƙata ba nasarar aikin ba, da sun samu sunan shikenan, aikin ba ya gaban su. Sai uwa uba rashin ilimi.

Da yawan ma’aikatan harkar shiyar fina-finai ta Kannywood da baiwarsu suke aikin ba wai da ilimi ba, amma kuma kuskuren da yawanci ake yi shi ne, idan harkar ilimin ta zo mu su sai su ƙi mai da hankali a kai su ƙara ilimin. Misali; wani ya shirya ‘workshop’ da za a ƙaru da ilimin harkar fim ɗin, kuɗin form dubu biyu ne kawai kuma za a ba da ‘certificate’, amma ba za su shiga ba. Wani kuma a gefe ya shirya ‘audition’ ya saka kuɗin form ɗin sa dubu biyu yadda za a yi tururuwar sayan form ɗin zai ba ka mamaki. Kaga rashin sanin ilimin harkar ne kuma ba a so a sani. Sai kuma rashin ƙin yarda da bin hanyoyin da suka dace a harkar, misali; ko da ga yanayin yadda ake ɗaukar aikin za ka ga da bambancin da yadda ake yi a duniya, sai ka ji wasu suna cewa ai ba mu kai wannan lokacin ba, wa ya gaya ma ka? Sai yaushe za mu kai?”

Da na buƙaci jin ta bakinsa ko ya yake ganin yiwuwar dawowar harkokin shirya fina-finai a Kannywood? Director Mansoor Sadiq sai ya ce, “Ina da tabbacin dawowar harkar shirya fina-finai, amma fa sai anbi hanyoyin da suka dace don harkar idan ta dawo ta tsaya da ƙafarta hanyoyin kuwa su ne; Tafiya da zamani, inganta ayyuka, haɓaka sinema da kuma hanyoyin sayar da fina-finai a duniya.”

Al’amarin kowa da irin yadda yake kallon cigaba ko akasin haka da masana’anar a yanzu take tafiya akai. Ibrahim Bala da yake zaman jami’in yaɗa labarai na ƙungiyar masu bayar da umarni a masana’antar kuma jarumi cewa ya yi, rashin samun kulawa da taimako daga gwamnati da manyan ƙasa ya sa masana’anatar ta durƙushe. Ya ƙara da cewa, kwata-kwata Kannywood ba ta samun duk wani haƙƙi da ya kamata a ce an ba ta, saɓanin takwarorin su na kudu.

Da na buƙaci jin ra’ayinsa game da ‘channel-channel’ na ‘YouTube’ da a halin yanzu ake ganin Kannywood ta nan kafar kawai ta ke motsawa. Sai ya ka da baki ya ce, “Buxe ‘YouTube’ a halin da masana’antar ta tsinci kanta a ciki na rashin madafa zan iya cewa an samu cigaba musamnan yadda wasu masu basira da ba su samu dama ba sun samu sun nuna kansu, kuma suna ɗan samun kuɗi daidai gwargwado.” 

Director Ibrahim Bala ya ƙara da cewa, “yadda zamani yake tafiya idan Kannywood ta samu damar da take buƙata na tallafi da kasuwancin zamani haƙiƙa za ta farfaɗo har tafi da. Kasuwancin zamani sai da kayan zamani ya ke tafiya.”

Shi kuwa Doctor Ahmad Bello Jarumi kuma guda cikin masu ruwa da tsaki a hakar fim ɗin Hausa kuma shugaban tsangayar koyar da harshen Hausa na FCE Zariya, cewa ya yi, saɓa wa ɗabi’a da al’adun Bahaushe shi ne umul’aba’isin durƙushewa harkar fim a masa’anatar Kannywood, domin Bahaushe bai ga wata gaɓa da aka wakilce shi ba sai ta harshensa. Ya ƙara da cewa, bayan wannan kuma akwai ƙyashi da baƙin ciki da ke kai kawo a tsakanin ‘yan masana’antar da suke yi wa junansu. Sai kuma waɗanda suka shigo masana’antar ba don Allah ba sai don buƙatar ƙashin kai. Sai kuma jahilci da rashin sani da ke tsakanin ‘yan Kannywood. A ɓangaren ‘Youtube’ kuma a ganin Malamin cigaba ne ga waɗanda duniyar fim ɗin ba ta san su ba, zuwa ‘YouTube’ ɗin ya sa idanuwa sun tsayu akan su.

Da na nemi jin ta bakinsa ko akwai yiyuwar dawowar masana’antar kamar da, sai ya ka da baki ya ce, “Abin da kamar wuya dawowar masana’atar kamar da. ‘Yan siyasa irinsu mai girma tsohon gwamnan Kano Malam IIbrahim Shekarau sun kassara fina-finan Hausa, kuma kar ka manta, Kano ce cibiya kuma mu’assa ta ɗaukacin harkar fim gaba ɗayanta.”

Kusan haka mafi yawa daga cikin ahalin wannan masana’atar ta Kannywood suke bayyana mabambantan ra’ayoyi game da dalilan da suka turmuza hancin masana’antar ƙasa, abin jira a gani shi ne, Kannywood ɗin za ta dawo kamar yadda wasu su ke da tabbaci ko kuwa akasin haka. 

Almustapha Adam Muhammad, marubucin fim kuma Darakta a masana’atar Kannywood kuma shi ne Sakatare a ƙungiyar Daraktoci ta Jihar Kano. [email protected]