Zamfara ta zama ta farko wajen tsara daftarin koyar da ilimin fasahar zamani a Nijeriya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamna Duuda Lawal na jihar Zamfara ya zama gwamna na farko da ya ƙaddamar da daftarin tsarin koyarwa harkokin fasahar zamani (ZDLF) domin bai wa al’ummarsa damar samun ƙwarewa da shiga a dama da su wajen bunƙasa tattalin arziƙi da tafi da harkokin gwamnati a zamanance da ƙirƙire-ƙirƙire.

An gudanar da babban taron masu ruwa da tsaki kan ƙaddamar da ga daftarin tsarin koyarwa na zamani ne a ranar Laraba a ɗakin taro na Garba Nadama Hall, a sakatariyar JB Yakubu da ke Gusau.

A cikin jawabin da mai magana da yawun gwamnan ya fitar, Sulaiman Bala Idris, ya ce taron ya tattara masu ruwa da tsaki daga manyan makarantun gwamnatin tarayya da abokan haɗin guiwa don samar da cigaba da ‘yan majalisu da masana ilimi da masu ruwa da tsaki a ɓangaren kamfanoni masu zaman kansu domin dubawa da ba da gudunmawa ga daftarin tsarin koyarwa na zamani.

A cikin jawabin nasa, gwamnan Lawal ya bayyana daftarin da zai zama jagora ga makomar al’umma kuma gwamnatinsa za ta tabbatar da ganin an aiwatar da wannan tsari.

Ya ce, “Yau rana ce babba ta nasara da zai sauya ba tsarin samun cigaba ga cigaban jihar Zamfara ta hanyar tallafawa harkar cigaban zamani da ƙirƙira da samun bayanai da sadarwa a fasahance.

“Daftarin Koyarwa ta hanyar zamani wani tsari ne na cika burin ilmantar da mutane ta tsarin zamani domin samun bunƙasa ta zamani.”

“Kamar yadda muka sani ne, ilimin tafi da harkokin zamani zai bunƙasa himma da ayyukan yi da ingantaccen tsarin hidimtawa. Ba za mu iya jure ganin al’ummarsu suna zama koma baya ba a harkar fasaha ta duniya.”

“Wannan dafatari zai ba da damar shigar da tsarin tafi da harkokin a zamanance da fasahar sadarwa cikin harkokin koyarwa da ayyukan gwamnati da kasuwanci. Muna son samar da jiha wacce kowanne ɗalibi zai samu ƙwarewa ta harkar fasaha da tabbatar da kowanne ma’aikaci ya samu ƙwarewar tafi da harkoki na zamani a ɓangaren aikin gwamnati da kasuwanci domin faɗaɗa kasuwanci. Kuma mun fara ƙoƙarin aiwatar da wannan tsari.”

“Jihar Zamfara ta haɗa kai da Oracle Corporation wajen ba wa matasa horo 3,000 a ɓangaren Cloud 2 Computing, da ƙirƙirarriyar basira da kimiyyar tattara bayanai da samar da ma’ajiyar tattara bayanai. Tare da taimakon Oracle Academy, dukkan manyan makarantu za su tallafa wa musu wajen samar da ƙwararrun ɗalibai da za su yi daidai da buƙatun masana’antu da muke da su.

“Tuni aka fara wannan aiki a cibiyar koyar da ilimin fasahar sadarwa (ZIIT) da ke Gusau. Wannan cibiya za ta zama matattara ta shiyya wajen samun ƙwarewa a ɓangaren ilimin fasahar sadarwa da haɓakar ƙirƙire-ƙirƙire a cikin gida. Muna son cike giɓin da ake da shi ne a ɓangaren harkoki na zamani ta yadda Zamfara za ta zama cibiya ta ilimin fasahar sadarwa a yankin Arewa.”

Tun da fari, a yayin da yake magana, sakataren gwamnatin Zamfara, Abubakar Nakwada, ya jaddada aniyar gwamnatin na maishe da jihar Zamfara kan gaba wajen kawo sauyi a ɓangaren ilimin fahasar zamani a yankin Arewa.

Shi ma sanata mai wakiltar Zamfara ta tsakiya, Ikra Aliyu Bilbis wanda shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin sadarwa da tattalin arziƙi na harkokin zamani a majalisar dattawa ya yaba jihar Zamfara na ɗaukar gabarar zama kan gaba wajen bai wa kowa damar samun ƙwarewa a ɓangaren fasahar zamani.

Sanatan ya ba da gudunmowar kwamfutoci 300 ga cibiyar bunƙasa fasaha (ZITDA) ta jihar domin tallafa wa yunƙurin kawo sauyi a fannin fasahar zamani.

A dunƙule daftarin koyar da ilimin fasaha ta jihar Zamfara (ZDLF), kamar yadda Dr Habib Gajam, babban sakatarencibiyar bunƙasa fasaha (ZITDA), ya bayyana, ya ce, wannan wani daftari ne da ka tsara don amfanar al’umma da nufin cimma abubuwa kusan guda 4 a matakin farko.

Sauran manyan makarantun koyar da ilimin fasaha da suka halarci taron sun haɗa da hukumar kula da sadarwa ta ƙasa (NCC), da kamfanin Galaɗy Backbone, da hukumar bunƙasa ilimin fasaha ta ƙasa (NITDA) da hukumar kula da tauraron ɗan’Adam ta ƙasa da hukumar kare haƙkin bayanai ta ƙasa (NDPC).

By ukarofi