Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wata sabuwar taƙaddama ta kunno kai a ƙarshen makon jiya yayin da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamiɗo ya zargi Shugaba Bola Tinubu da kasancewa mai goyon bayan soke zaɓen Shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993.
Marigayi Bashorun Moshood Abiola, ɗan takarar shugaban ƙasa na SDP shine wanda ake kyautata zaton ya lashe zaɓen da gwamnatin mulkin soja ƙarƙashin jagorancin Janar Ibrahim Babangida ta soke, wanda Lamiɗo shi ne sakataren SDP na ƙasa a lokacin.
Da yake magana a gidan talabijin na Arise Tɓ, wanda faifan bidiyonsa ya bazu, Lamiɗo ya bayyana mamakinsa kan iƙirarin da Shugaba Tinubu ya yi na cewa shi mai adawa ne da soke zaɓen 12 ga watan Yuni.
Kamar yadda wani kwafin faifan bidiyon Arise Tɓ ta The Conclaɓe, Lamiɗo ya ce: “Na ji daɗin kalaman Tinubu, yadda yake nuna rawar da ya taka a dimokuraɗiyyar Nijeriya.
To sai dai kuma Fadar Shugaban ƙasar Nijeriya ta ita ma ta kai ga jin waɗannan kalamai da tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamiɗo ya yi.
“Wannan zargi da Lamiɗo ya yi ƙoƙari ne na sauya abin da ba haka yake ba a tarihance,” cewar fadar shugaban ƙasar.
Ya zargi cewa Shugaba Tinubu ya yi suna ne bayan kafa ƙungiyar fafutukar neman Abacha ya sauka daga shugabancin Nijeriya ya bai wa Abiola wanda ake ganin shi ne ya lashe zaɓen 1993 da ake kira da NADECO da cewa mahaifiyar Tinubu, Abibatu Mogaji, ita ce ta tattara mata da ke kasuwa domin mara wa fafutukar ƙin jinin soke zaɓen. Waɗannan zarge-zage ƙarya ne.
Bari mu yi bayanin abin yadda yake: Mahaifiyar Tinubu, Mrs Mogaji ba ta taɓa tattara kan mata da ke kasuwa domin mara wa kiran rashin adalci ba bayan soke zaɓen 1993. Da a ce ta yi hakan, da ta rasa muƙaminta na zama shugabar kasuwar a Legas. Duk da cewa ta samu wata alaƙa da shugaban ƙasa na wannan lokaci, Babangida, amma wannan alaƙar kafin a soke zaɓen ne.
Yana da kyau a tuna wa ‘yan Nijeriya cewa, Lamiɗo, a matsayin sakataren jam’iyyar SDP — jam’iyyar da ɗan takararta ake iƙirarin shi ne ya lashe zaɓen, MKO Abiola, yana cikin waɗanda suka ƙi ƙalubalantar gwamnatin mulkin sojin bayan soke zaɓen. Shugabancin jam’iyyar SDP wanda ya haɗa da shi Lamiɗo da shugaban jam’iyyar Tony Anenih, sun sa hannu kan takardar da ta miƙa haƙƙin al’umma ba tare da turjiya ba. Kuma su ne suka haɗa kai da wata ƙungiya National Republican Conɓention wajen hana Abiola zaɓen da ya lashe.
Sai dai bambancin da ke akwai shi ne, shi Bola Tinubu ya tashi tsaye ya ƙalubalanci soke zaɓen tun ma kafin Abacha ya rufe jam’iyyun siyasa wanda ya haɗa da majalisa ta Nijeriya a ranar 17 ga Nuwambar 1993 bayan juyin mulki da Abacha ya yi.
Kwanaki kafin Babangida ya sanar da majalisa aniyarsa ta ajiye muƙaminsa a ranar 27 ga watan Agustan 1993, tare da kafa gwamnatin riƙon ƙwarya da za ta maye gurbinsa, sanatoci sun yi muhawara kan jawabin nasa. A ranar 19 ga Agustarn1993 ne, Tinubu ya yi Alla-wadai da soke zaɓen yana mai bayyana hakan da wani salo na juyin mulki kuma lallai ‘yan Nijeriya su yi watsi da rashin adalcin.
Wannan ya nuna cewa Tinubu ya nuna goyon bayansa ga zaɓen 12 ga Yunin 1993 saɓanin shi Lamiɗo wanda bai yi hakan ba.
“Muna da tunanin cewa soke zaɓen da aka yi na 12 ga wata wani juyin mulkin ne,” inji Tinubu.
“Tambayata ita ce, har zuwa yaushe za mu cigaba da karɓar irin wannan rashin adalcin da juyin mulki da take haƙƙin mutanen da aka kashe kuɗinsu a ƙasar nan? E, tabbas an samu rikice-rikice amma akwai wanne irin mataki da aka ɗauka akwai sakamako. Ba za a samu rikici ba inda ba a soke zaɓen ranar 12 ga watan Yuni ba. Muna da gwamnati ne mai taka dokar da ita ta samar. Don haka, wannan gwamnati ta mulkin soja, idan aka yi la’akari da yadda ta take dokar da ita da kanta ta yi su, ta aikata laifi,” a cewar Sanata daga Yammacin jihar Legas.
Abiola a lokacin da majalisa ta yi zamanta kan kalaman Babangida na kafa gwamnatin riƙon ƙwarya, Abiola ba ya ƙasar. Ya dawo Nijeriya ne a watan Satumba, 1993 kuma waye ke take ma Abiola baya a lokacin da Abacha ke kitsa yuyin mulki ga gwamnatin Ernest Shonekan? Tinubu ne. Akwai hotuna da dama da ke nuna Tinubu tsaye a bayan Abiola.
Abacha ya karɓi mulki ne a ranar 17 ga watan Nuwambar 1993 tare da rushe dukkan jam’iyyun siyasa da gwamnoni da ‘yan majalisun tarayya da na jihohi. A lokacin ne Tinubu da wasu sanatoci suka taru a Legas domin ƙalubalantar Abacha. Tinubu, Ameh Ebute, Abu Ibrahim da sauransu an kama su, an kuma ajiye a Alagbon. ‘Yan sanda sun kai su kotu, aka ƙirƙiri laifi na ƙarya. A lokacin da suke tsare, Tinubu ya cigaba da ɗaukar nauyin masu zanga-zangar ranar 12 watan Yuni wanda ya kai ga rufe Babbar gada ta uku (Third Mainland Bridge).
Bayan wasu makonni ne, Abacha ya ɗauki wasu matakai da suka tabbatar wa da Abiola da Tinubu cewa shi ba soja ne mai son dimokraɗiyya ba, balle kuma dawo wa da Abiola zaɓensa.
A ranar 15 gawatan Mayun 1994 aka kafa ƙungiar NADECO wacce ta ƙunshi ‘yan Nijeriya masu kishin dimokraɗiyya a Nijeriya wacce ta riƙa yin kira ga gwamnatin Abacha kan ta sauka ya miƙa wa wanda ya lashe zaɓen 12 ga Yunin 1993, MKO Abiola. Bayan cika shekara ɗaya da zaɓensa, Abiola ya gudanar da jawabi a Epetedo a jihar Legas inda ya ayyana kansa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa. Bayan kwanaki 10 a ranar 22 ga Yunin aka kama shi wanda daga nan ne da yawan masu rajin kare dimukraɗiyya suka yi gudun hijira daga Nijeriya kuma ciki har da Bola Tinubu. Tinubu ya zauna a ƙasar waje na kusan shekaru 5 a yayin da Lamiɗo da makamantansu suka ƙulla alaƙa da Abacha. A lokacin da Tinubu baya ƙasar nan, wasu daga cikin gwamnatin mulkin soji, sun ƙone gidansa da ke Balarabe Musa Crescent, Victoria Island.
“Mun gode da Lamiɗo ya ce, Tinubu ya taka muhimmiyar rawa a NADECO. Tabbas Tinubu ya yi abubuwa da yawa. Ya kuma mara wa tafiyar Farfesa Wole Soyinka ta NALICON, wanda ya taimaka wa tafiyar tasa.
“Sanannen abu ne cewa, Tinubu ya taka rawa wajen fafutukar da aka yi bayan soke zaɓen 12 ga watan Yuni. Da yawan shugabannin NADECO da ‘yan jaridu da suka yi gudun hijira da waɗanda suke zaune a Nijeriya, Tinubu ne ya cigaba da ɗaukar nauyinsu da kuɗin cigaba da fafutukar da suke yi.
“Da wannan labari, Lamiɗo bai ma san irin gudunmmuwar da NADECO ta bayar ba wadda ta samo asali bayan rikicin zaɓen 12 ga watan Yuni.
“Abin takaici ne duk da sanin irin gudunmmuwar da Tinubu ya bayar, Lamiɗo na ƙoƙarin sauya labarin tarihi saboda dalilai na siyasa.
“Muna ba wa Lamiɗo shawara da ya sake duba hujjojinsa kafin ya shiga gidan talabijin wajen yaɗa ƙarya. Wannan ba zai taimake shi ba da tafiyar da yake yi.
“Mun kasa yadda da ko Lamiɗo na fama da wata cuta ta tunani da ake kira da “poppy syndrome”, sai dai ƙarshe a fili yake cewa Lamiɗo na yin hassada ga Tinubu ne. A fili yake cewa Tinubu har zuwa yau yana ƙoƙarin kare dimokraɗiyya saɓanin Lamiɗo da sauran waɗanda suka ribaci cin zarafin gwamnatin mulkin soja.”
