Zan koya wa sauran jam’iyyun darasi a 2023, cewar Fintiri

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Adama, Ahmad Fintiri ya ce zai koya wa sauran jam’iyyun siyasa darussa a zaɓen 2023 idan Allah ya kaimu.

Fintiri ya bayyana haka ne a lokacin amincewarsa da ƙungiyar kansilolin jihar Adamawa a ɗakin liyafa na gidan gwamnati da ke Yola a ranar Laraba 1 ga watan Disamba. 

A wajen gagarumin taron, an jiyo gwamnan jihar Adamawa yana cewa, “a tsayar da ɗan yankin shugabancin ƙasa a zauna lafiya, inda ya ce ya bayyana cewa ta kowane ɓangare jam’iyyar APC ta gaza cika wa ‘yan ƙasa tarin alƙawuran da suka ɗauka musu. Haka zalika sun gaza a shekarun baya da suka samu damar da gudanar da mulki a jihar ta Adamawa.

“Sun gaza a cikin shekaru huɗu da suka samu damar gudanar da mulkin jihar, kuma ba za mu bar su su yaudari jama’ar mu ba, za mu ci gaba da yin aiki tuƙuru, mu samar da romon dimokuraɗiyya. 

“A kan haka, na yi imanin, za mu koya musu darussa munana cewa za su rasa dukkan zaɓuka tun daga kan shugaban ƙasa zuwa matsayi na ƙarshe a cikin al’umma, wato na kansila.” 

A zaɓen gwamnan jihar Adamawa na 2019, Fintiri ya samu ƙuri’u 376,552, inda ya doke Jibrilla Bindow, gwamna mai ci kuma ɗan takarar jam’iyyar APC, wanda ya samu ƙuri’u 336,386. 

“Shugaba nagari muke so ba ɗan kama-karya ba,” cewar Gwamna Fintiri lokacin da ya halarci wani taron siyasa cikin watan Oktoba 202I. Haka kuma Fintiri ya bayyana cewa, ‘yan Nijeriya na buƙatar shugabanni masu nagarta ba tare da duba kabila ko addininsu ba. 

“Matsalar Nijeriya ba ta tsarin shiyya-shiyya ba ce, ya rage namu mu nemo ɗan takara mai inganci. Duk inda wannan mutumin ya fito, ba tare da la’akari da addininsa ko ƙabilarsa ba. 
“Abin da ni da ku muke fata a yau shi ne samun shugaba nagari wanda zai iya samar da ci gaban tattalin arzikin mu, tsaro wanda zai yi tasiri ga ci gaban bil’adama, samar da irin kayayyakin more rayuwa da muke buƙata.” 

A ɓangare guda kuma, Ahmadu Fintiri, ya ce zai mara wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar baya idan ya sake tsayawa takarar shugabancin Nijeriya a jam’iyyar PDP a zaven 2023.

Manhaja ta tattaro cewa, Fintiri wanda shi ne shugaban kwamitin taron gangamin jam’iyyar PDP na ƙasa ya bayyana haka ne a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba, a lokacin da ya bayyana a matsayin baƙo a gidan talabijin na Channels TV a shirin Politics Today. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *