Zan yi aiki da Sweden don cigaban Zamfara – Lawal

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce a shirye yake ya yi aiki tare da ƙasar Sweden wajen bunƙasa ɓangarorin jihar.

Ya ce fannonin jihar da za a bunƙasa sakamakon haɗin kan sun haɗa da harkar haƙar ma’adinai, fannin noma, ilimi da kuma ɓangaren makamashi.

Gwamna Lawal ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Jakadiyar Sweden a Nijeriya, Annika Hahn-Englund a ofishinsa da ke Abuja a makon da ya gabata.

Sanarwa mai ɗauke da sa hannun Mai Magana da Yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris, wadda aka fitar a ranar Lahadi, ta ce ziyarar Jakadiyar ta bai wa ɓangarorin biyu tattauna yadda za su ƙaru da juna.

A cewar sanarwar, Gwamna Lawal ya shirya yin amfani da dukkan hanyoyin da suka kamata wajen jayo masu zuba jari a jihar da kuma gudunmawa daga abokan hulɗa daga ƙetare.

“A makon da ya gabata Gwamna Dauda Lawal ya karɓi baƙuncin Jakadiyar Ƙasar Sweden, Annika Hahn-Englund a ofishinsa da ke Abuja.

“Tattaunawarsu ta maida hankali ne kan yadda za a ƙulla ƙawancen da za ta taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar Zamfara da aiwatar da ayyukan cigaba don amfanin jihar da al’ummarta,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, yayin ganawar Gwamna Lawal ya bai wa baƙuwar tasa tabbacin samun haɗin kan gwamnatinsa domin kawo cigaba a fannoni daban-daban.

By Editor