
Daga Sanusi Muhammad a Gusau
Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara, ta yaba wa Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar da Ƙaramin Ministan Tsaro, Hon. Bello Muhammad Matawalle bisa jajircewa da su ka yi wajen ganin babu wani ɗan Jam’iyyar da ya shiga zanga-zangar da aka gudanar a ranar Alhamis a jihar.
Sakataren yaɗa Labarai na jihar, Yusuf Idris tare da ɗaukacin shugabannin jam’iyyar na jihar su ka bayyana hakan a wani taron manema labarai da su ka gudanar a babban masauƙin baƙi mallakar rundunar soji (Command Guest Inn) da ke Gusau a ranar Juma’a.
Sun bayyana ƙoƙarin da Sanata Yari da Matawalle suka yi a matsayin abin maraba da kuma cigaba.
“Tun da farko, mun yi hasashe kan yiwuwar ɓarkewar hargitsi a zanga-zangar da aka gudanar a jihar, hakan yasa ɗaya daga cikin jagororin Jam’iyyarmu, Mai Girma Abdulaziz Yari Abubakar ya gana da shugabannin jam’iyyar tun daga ƙananan hukumomi har zuwa jiha da sauran masu-ruwa-da-tsaki tare da bayyana mu su cewa shi da Ministan tsaro, Bello Muhammed Matawalle babu hannunsu a zanga-zangar tare da umartar duk ɗan Jam’iyyar APC a Zamfara da ya ƙaurace mata, hakan kuma akayi”, inji Idris.
Ya ƙara da cewa “Sanata Yari da Matawalle sun kuma yi kira ga kowa da kowa da su kasance masu bin doka da oda domin ɗorewar zaman lafiya da cigaban jihar da ƙasa baki ɗaya. Mu na so mu fayyace cewa babu wani ɗan APC da ya shiga yajin aiki da ake shirin yi a faɗin jihar Zamfara.”
APC ta roƙi jami’an tsaro a jihar da su bai wa mambobinsu da duk ƴan ƙasa masu kishi kariya da ake buƙata a rayuka da dukiyoyinsu a halin da ake ciki na gudanar da zanga-zanga a ƙasa baki ɗaya.
Shugabannin jam’iyyar sun kuma bayyana rashin jin daɗinsu kan yunƙurin ƙone gidan tsohon gwamna kuma Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Muhammed Matawalle a Gusau da kuma gidan Sanata Sahabi Ya’u da ke garin Ƙauran Namoda wanda su ke zargin ƴan bangar siyasar Jam’iyyar PDP ne su ka yi a yayin gudanar da zanga-zanga a jiya Alhamis.
Sun kuma yaba wa jami’an tsaro da su ka yi gaggawar mayar da martani ta hanyar hana ƴan bangar siyasar kai farmakin a gidan Matawalle da ke Gusau a lokacin zanga-zangar.
“Idan ba don gaggawar mayar da martani da sojoji su ka yi ba, da ƴan bangar siyasar sun sanya wa gidan Ministan wuta a yayin zanga-zangar”, inji Sakataren.
Har’ilayau, APC ta yi kira ga magoya bayanta da mambobinta na Zamfara da su zamo masu bin doka da oda tare da mara wa gwamnatin tarayya baya don samar da cigaba a jihar da ƙasa baki ɗaya.
