Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jami’an DSS a Katsina sun kama ɗan gwagwarmaya Kabir Shehu ‘Yanɗaki, wanda shine sakataren gamayyar ƙungiyoyin farar hula ta ƙasa.
Shi wannan ɗan gwagwarmaya shi ya jagoranci zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a Jihar Katsina ranar Alhamis.
Babu wani cikakken bayani daga hukumar tsaron game da kamen nashi.
Sai dai ba zai rasa nasaba da irin yadda masu zanga-zangar suka lalata kayayyakin gwamnati da ɓalle shagunan mutane suka yi ta wasoso ba.
A halin yanzu dai al’amura sun fara dawowa yadda suke, domin ‘yan kasuwa sun fara buɗe shagunansu a hankali, ga zirga-zirgar ababen hawa ba fargaba.
Faɗin jihar dai babu wani rahoton zanga-zanga, jami’an tsaro ne kawai ke ta kaiwa da komowa a ciki da kewayen garin Katsina da sauran manyan birane a jihar.
Sai da jami’in yaɗa labarai na rundunar ‘yan sanda a Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar da kama wasu ɓata-gari 50.
“Da zaran an gama bincike za a gurfanar da su a kotu,” inji shi.
