Zanga-zanga ta kashe ma na kasuwa, inji mabaratan Kano

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO

Wasu masu yawon barace-barace a kan titinan birnin Kano sun koka ga masu shirya zanga-zanga a faɗin Nijeriya da cewa, su mayar da wuƙarsu cikin ƙube, don nuna jinƙai a gare su, su na masu cewa, zanga-zangar da ake gudanarwa a faɗin ƙasar ta kashe kasuwarsu bakiɗaya. A cewarsu, akasarin masu bara a ƙasar su na samun abinda za su ci ne kawai, idan sun fito yawon bara kullum, inda yanzu haka zanga-zangar ta hana su sakat.

An fara zanga-zanga a Nijeriya ne ranar 1 ga Agusta, 2024, don yin matsin lamba ga gwamnati kan halin matsin rayuwa da ’yan Nijeriya suka tsinci kansu a ciki sakamakon tsadar kayayyaki da yunwa da suka ta’azzara a faɗin ƙasar.

Wani dattijo mai shekaru 70 da ke yawon bara a unguwar Rijiyar Zaki da ke Kano mai suna Baba Halliru ya shaida cewa, sakamakon wannan fito-na-fito da ake yi a Nijeriya yanzu rayuwa ta ƙara ta’azzara a gare su, yana mai kukan cewa, “ba mu ci abinci a gidanmu ba yau kwana biyu kuma mu guda 14 ne a gidan, sai ruwa kawai mu ke iya sha. Don Allah ku tuntuɓi masu shirya zanga-zangar nan da su tsahirta haka nan ta hanyar cimma masalaha da gwamnati.”

Su ma wasu mabaratan sun bayyana ra’ayi irin nan Baba Halliru, su na masu kira da a kawo ƙarshen zanga-zangar da ma dokar hana fita da aka ƙaƙaba a gari.

Malama Mairo Kabiru da ke unguwar Hotoro ta ce, “abincinmu ya ƙare kuma ba za mu iya sayen wani ba, saboda ba mu da kuɗi. Yanayin ya kai munzalin intaha.”

Malam Isa Musa na unguwar Dorayi shi kuma ya yi roƙo ga gwamnati da ta fito da wasu hanyoyi na tallafa wa tsofaffi marasa galihu ne.

Ya ce, “mu na yin bara ne, saboda ba mu da wanda zai taimake mu. Tun da aka ƙaƙaba dokar fita ba mu ci komai ba tsawon kwanaki uku mu da iyalanmu. Ba za mu iya ci gaba da rayuwa a haka ba. Ku taimaka ku cewa masu zanga-zangar nan su dakata haka.”

Sai dai kuma, zafin zanga-zangar ya ragu har ma al’amura sun fara koma wa daidai bayan da tun da fari ta rikiɗe ta koma tashin hankali, inda aka samu rahotannin asarar rayuka a wasu jihohi, lamarin da ya tilasta wa gwamnatocin jihohi kamar Kano, Kaduna, Katsina, Borno, Neja da sauransu sanya dokar hana zirga-zirga.

Haka nan, jami’an tsaro sun kama wasu daga cikin jagororin zanga-zangar, yayin da wasu kuma suka arce, suka kashe wayoyinsu. Lamarin ya kai tsamarin da har ’yan ƙasar Poland aka kama a yayin da ake gudanar da zanga-zangar a Kano ranar Talatar da ta gabata.

Kafin abin ya lafa, an ga wasu daga cikin masu zanga-zangar a hotunan bidiyo su na fasa shagunan mutane suna kwashe kaya a ciki, lamarin da ya janyo tir da allawadai daga masu lura da al’amuran yau da kullum.

Sai dai kuma an zargi wasu jami’an tsaro da yin amfani da ƙarfin da wuce kima, inda hukumar kare haƙƙin bil’adama ta Majalisar ɗinkin Duniya, Amnesty International, ta yi kira da a gudanar da bincike kan lamarin kashe-kashen.

By ukarofi