Atiku ya soki Gwamnatin Tinubu kan yaɗa farfagandar ruɗar al’umma

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Tawagar yaɗa labaru na tsohon shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ta soki tsarin isar da saƙo na gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ga ƴan Nijeriya, ta na mai zargin hakan a matsayin farfagandar ruɗar al’umma.

Hakan na zuwa ne bayan da aka yaɗa wani tsohon bidiyo na shugaba Tinubu ta kafar X inda ya ke lallashin al’umma domin kare kasawar gwamnatinsa la’akari da zanga-zangar tsadar rayuwa da ake yi a faɗin Nijeriya.

Asalin bidiyon an yin shi ne tun kafin wannan lokacin wanda tawagar ta ke ganin hakan a matsayin salo na wasa da hankulan al’ummar ƙasa daga ofishin.

Cikin sanarwa da mai taimaka wa Atiku kan harkokin labaru, Paul Ibe ya fitar, ya caccaki al’amarin, ya na mai cewa hakan yaudarar al’umma ce.

Ibe ya kuma soki tsare-tsaren yaɗa labarai na gwamnatin Tinubu da ya fassara da wani salo ne da ka iya rage yarda da kuma aminci da ke tsakaninta da al’umma.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin da ta gaggauta fitowa ta bayar da haƙuri ga al’umma kan ruɗar su da ta yi wajen isar da saƙon wasa da hankulansu, ya na mai cewa ƴan ƙasa sun cancanci a yi mu su hakan.

By Babaji