Zargin fyaɗe: An garƙame makarantun islamiyya biyu a Kaduna

Daga WAKILINMU

Hukumar Kula da Ingancin Makarantun na jihar Kaduna (KSSQA), a makon da ya gabata ta rufe makarantun Islamiyya biyu a jihar har sai masha Allahu kan zargin yi wa ɗalibai fyaɗe da yi wa wata ɗalibar ciki.

An rufe ɗaya daga cikin makarantun mai suna Madrasatul Ulumul Deeniya wa Tahfizul Qur’an a Rigasa ne kan zargin yi wa wata yarinya mai shekaru shida fyaɗe a harabar makarantar.

Ɗayan makarantar Islamiyyar kuma tana Tsohon Masallacin Juma’a ne na Kachia, a ƙaramar hukumar Kachia na jihar Kaduna, shi ma an rufe shi ka zargin wani mallami mai shekaru 50 da yi wa ɗaliba mai shekaru 12 ciki.

Daraktan KSSQA, Mr Idris Aliyu, wanda ya umarci a rufe Islamiyyar da ke Rigasa ya bayyana yadda aka ci zarafin ’yar shekara shida a harabar makarantar kuma hukumar makarantar ta rufe maganar inda ta nuna kamar ba ta san hakan ya auku ba.

A cewar Aliyu, ma’aikatar ta samu bayanai akan yadda kakar yarinyar ta kai ƙorafi makarantar amma ɗalibai da malaman Islamiyyar suka zane ta.

Don haka a cewarsa, Gwamna Nasir El-Rufai ya umarci a rufe Islamiyyar har sai an kammala bincike akan lamarin kuma an kama wanda ya yi aika-aikar.

Aliyu ya ce, “yanzu dai shugaban makarantar za a kama da laifin aika-aikar har sai yarinyar ta nuna wanda ya yi mata fyaɗe kuma an yanke masa hukunci. Duk wanda ya daki kakar yarinyar sai ya ɗanɗana kuɗarsa, musamman shugaban makarantar don aikin gwamnatin jihar ne kare haƙƙin wanda aka zalunta.”

Shugaban makarantar, Malam Kabir Abdullahi ya musanta zargin inda ya ce, ba fyaɗe bane. Ya ce, yarinyar ce ta cusa sanda a al’aurarta.

A cewar Abdullahi, yanzu haka DPO ɗin Rigasa, ASP Abubakar Bauranya ya kammala bincike akan lamarin.

DPO ɗin ya tabbatar da batun shugaban makarantar Islamiyyar. Sai dai kakar yarinyar, Hajiya Batul Gambo ta ce, fyaɗe aka yiwa jikarta kuma ta tabbatar da hakan bayan ta garzaya Asibitin Yusuf Ɗantsoho da ke Tudun Wada Kaduna.

Wata takardar asibiti wacce Dr A Raji ya sa hannu, ta nuna cewa, tabbas fyaɗe aka yi wa yarinya, a cewar kakarta.

Rahoton Raji ya nuna cewa, al’aurarta ta ji rauni sannan kuma an kawar da budurcinta.

Batun yarinya mai shekaru 12 da aka yi wa ciki a Kachia, Aliyu ya ce, yanzu haka tana da ciki wata shida. A cewarsa, an rufe Islamiyyar bisa umarnin El-Rufai, inda ya ce, ba za a yi wasa da lafiyar ɗalibai ba.

Ya ce, kwamishinan harkokin jama’a da ci gaba, Hajiya Hafsat Baba da kwamishinan ilimi, Hajiya Halima Lawal za su yi aiki tare da ’yan sanda wurin bincike da tabbatar da adalci ga waɗanda aka zalinta.

“Za a ci gaba da garƙame makarantun har sai an kammala bincike kuma an hukunta waɗanda su ka yi laifin yadda shari’a ta tanadar,” a cewarsa.