Yadda Birrai suka fusata suka kashe karnuka 250

Birrai a wani birnin Indiya sun kashe karnuka 250, tare da jefo su daga saman manyan benaye da bishiyoyi, kamar yadda kafar labarai ta News18 ta ruwaito.

Mazauna yankin Labool, wani gari ne mai kimanin mutum 5,000 da ke da nisan mil 300 a gabas da birnin Mumbai, sun shaida wa News18 cewa, birrai sun fara ɗaukar fansa ne a watan jiya bayan da wasu karnuka suka kashe wani ɗan biri ɗaya.

Mazauna yankin sun ce, tun daga lokacin ne birrai suka fara farautar karnuka ta yadda da zarar sun hango su sai su ja su zuwa saman dogayen gine-gine ko bishiyoyin suna jefo su ƙasa don hallaka su.

Birran sukan jefo karnukan ne daga sama, kamar yadda kafar labarai ta News18 ta ruwaito, har sai sun mutu.

Kafar labarai ta Newsweek ta ruwaito cewa, kusan kowane kare a garin an kashe shi.

Newsweek ta ce, an kira jami’ai daga Sashen Kula da Dazuzzuka a yankin don su taimaka wajen kama birran, amma ba su iya kama ko ɗaya ba. Daga nan ne mazauna ƙauyukan suka yi ƙoƙarin kama birran.

News18, ta ce, da yawa daga cikin birran sun samu raunuka a ƙoƙarin kisan karnukan.

“Birrai a yanzu suna kai hari kan ƙananan karnuka, suna haifar da firgici a yankin Labool,” kamar yadda News 18 ta ruwaito.

Mataimakin Farfesa a Jami’ar SUNY Buffalo, Stephanie Poindedter, wanda bincikensa ya mayar da hankali a kan halayyar halittu waɗanda suke da tafin hannu, tafin kafa da kuma fuska mai ɗauke da idanu da suke fuska kamar ɗan Adam da birrai, ya ce, “a cikin binciken da aka yi game da irin waɗannan halittu da ake killacewa, a cikin wuraren da jama’a ke ziyarta kamar gidajen namun daji, mun gano cewa lokacin da aka kai wa irin halittun hari ta wata hanya.

“Akwai yiwuwar su mai da martani ta hanyar kai hari ga wanda ke da alaƙa da wanda ya zalunce su, kuma martanin zai fi tsanani fiye da yadda aka kai masu.”