Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI
’Yan uwa masu karatu, Assalamu alaikum. Barkanmu da wannan lokaci, barkanmu da sake saduwa a wannan shafi da ke kawo mu ku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. A yi min afuwa na shiru da a ka ji, hakan ya faru ne sakamakon tarin ayyuka da su ka yi min yawa. Amma yanzu alhamdulillah!
Duba da lokacin da muke ciki yanzu, wato lokacin hunturu, rubutun yau zai mayar da hankali wajen bayani akan yadda jikin dan adam ke gudanar da al’amuransa lokacin sanyi; da kuma shawarwari kan yadda mutum ya kamata ya kula da kansa a wannan yanayi. Idan kun shirya, my je zuwa.
A duk lokacin da yanayi ya canza, to shima jikin ɗan adam ya na canzawa, domin tafiya da wannan yanayi ta yadda jikin ba zai cutu ba. Wannan shi ne yadda Gwani mai tsara halitta ya gina jikin mutum, yadda kasan wata na’ura mai sarrafa kwanta (abinda nature ya ke Kira da “automatic”.
Wataƙila mafi yawan mutane abinda su ka fi sani shi ne sanyi na damunsu a hannu da kafafu; kunnuwansu, wuyansu da idanunsu. Fiye da haka, jikinka da nawa ya na jin sanyi kuma ya na daukar matakai na yadda zai kare kansa daga illar Sangin ta hanyar rage jin sanyin. Amma ba kowa ne yasan da hakan ba.
Abin tambayar a nan shi ne: Wai da farko ma, ya ma ake kasan kana jin sanyi?
Jin sanyi yana faruwa ne a lokacin da jijiyoyin motsi na laaka da suke ɗamfare a jikin fata suka fahimci cewa iskar sanyi ta bugi fata. Daga nan sai su dauki sako izuwa ƙwaƙwalwa cewa: “sanyi fa ya bugi fatar jiki”; to daga nan sai ƙwaƙwalwa ta fassara saƙon da cewa sanyi ya sauka akan fatar, tare da aiko umarnin hukuncin da ya kamata a dauka: shin da bargo zaki rufa? Ko rigar sanyi zaka sanya? Ko hancinka zaka toshe? Ko ɗaki za a shige domin rage jin sanyin?
Ƙwaƙwalwarka ta na ɗaukar matakai na ciki da na waje domin kare ka/ki daga illolin sanyi. Matakai na waje sun haɗar da rufe ƙofa da tagogi, sanya riguna jibga-jibga masu rage ratsawa da shigar sanyi cikin jikinmu da kuma samar mana da ɗumi, sanya safa ta hannu da ta kafa, hular sanyi da sauransu.
Idan ku kayi tunani, su kansu wadannan matakai da muke ganin cewa na waje ne, sun samo asali ne daga sassa guda biyu na ƙwaƙwalwa: ɗaya ana ce masa “cerebral corteks”, ɗayan kuma ana ce masa “limbic system”. Haɗin gwuiwar waɗannan sassan guda biyu na ƙwaƙwalwa shi ne ke fayyace irin sanyin da zamu ji.
“Cerebral corteks” cibiya ce mai sarrafa hankalin ɗan adam. Idan mutum yazo bakin titi zai tallata yaga Motoci na wucewa, ai zai Dakata su tsagaita; idan mutum tafasasshen ruwa, ai ba zai soma tsoma hannunsa ba! A irin waɗannan misali, wannan koteks ke aiki. “Limbic system” kuwa cibiya ce ta da ke kula da yadda muke jin yanayin jikinmu (misali murna, fushi, jin zafi, ko jin sanyi, da sauransu). A duk lokacin da wani ya dame mu da surutu, ko wani ya zagemu, ko ya yi wani abu da zai sa ranmu ya sosu, wato mu shiga cikin yanayin da bature ke Kira “emotional feelings “, to haƙiƙa a wannan lokaci, “limbic system” ke aiki.
Yadda waɗannan cibiyoyi suka fassara abin ke fuskantarmu, haka halayyarmu za ta kasance a zahirance. Idan wani zai daure ya fita a cikin muku-mukun sanyi izuwa shago ko ofis, cibiyoyin nan guda biyu su ne a bakin aiki. Ku kalli mahaukaci mana, da yake cibiyar hankali dake ƙwaƙwalwarsa bata aiki, sai kuga yana ta yawo cikin sanyi abinsa.
Yanzu bari muga matakai na ciki. Babban matakin da jiki ke ɗauka yayin da sanyi ya buge shi, shi ne taskance zafin jiki domin a dumama shi kada sanyin gari yayi masa illa. Akwai hanyoyi da matakai da jikinmu ke ɗauka wajen taskance zafin da ke cikin jiki, don hana shi fita da mayar da shi makamashin ɗumama jiki! Wani aikin sai Jalla Gwani!
Jikinka zai rage yawan jinin da ke zuwa sassa daban daban na jiki ta hanyar tsuke jijiyoyin da jini ke gudana. Hanyoyin jini da ke kasan fatarki ko fatarka suna ɗauke da jini mai ɗumi ne. A tsarin aikin jikin ɗan adam, wannan ɗumi da jinin ke ɗauke da shi, da zarar ya kusanci fata sai dumin ya sirare ya fita da hudojin gashi dake fata, tare da gumi. Ta haka jiki yake rage zafin da ke cikinsa.
To a lokacin sanyi, jikinmu yana son wannan dumi da jinin ke ɗauke da shi, saboda haka sai jiki ya yi ƙoƙarin rage yawan jinin da ke biyowa hanyoyin jini na karkashin fatarka ko fatarki. Ana farawa ne ta kan jijiyoyin jinin da ke ƙarƙashin fatar hannaye, da ‘yan yatsu, da kuma ƙafafu da yatsunta, saboda su ne a buɗe mafi yawan lokaci, wanda hakan ya bayu izuwa sallamar da sanyi ke musu a kowanne lokaci. To tunda jini mai ɗumi ya rage zuwa ƙarƙashin fatar hannu da ta ƙafa, hakan sai ya sa mu dinga jin sanyi a hannayenmu da ƙafafuwanmu fiye da sauran sassan jiki.
A dunƙule, shi jikin mutum kamar mashin yake; yayin da sanyi ya busa, yanayin ɗumamar Hari ko zafin gari ya ragu, sai jiki ya ririta ɗumin da yake dashi a wannan yanayi. Yayin da aka samu akasin hakan to jiki zai dinga bari ɗumin da ke cikinsa ya dinga fita.
A lokacin hunturun santi, daga ayyukan da ke faruwa a jikin ɗan adam, ƙwaƙwalwarka za ta dinga angiza tsokar jiki ta dinga motsawa da sauri sauri. Wannan shi ake kira rawar ɗari. Amfanin hakan shi ne samar da zafi wanda zai ɗumama jiki. A duk sanda wata gaɗa ke aiki a jikin mutum, to zafi na samuwa ta ciki; kamar yadda idan ka kunna wata na’ura zafi zai samu. Wannan yawan mammotsawar tsoka cikin sauri lokacin da mutum ke rawar ɗari ita ce hanyar da jiki ke samarwa da kansa ɗumi.
Kenan ashe jikin mutum yana aiki iri biyu a nan: Alkinta ɗumin jiki, da kuma samar da dumin jiki. Wannan wata rahama ce daga Rabbul Izzati! Domin kulawa don kada ɗumin da ke cikin jiki yayi ƙasa, akwai ‘yan aike masu matuƙar saurin fahimtar sauyin yanayi da ke karkashin fatarka: idan an mintsineka, ko an yakusheka, ko ka taka wani abu, da sauri za su sanar da ƙwaƙwalwa cewa ga abin ke faruwa.
A yayin jin sanyi, zasu dauki sakon cewa sanyi ya bugi fata sukai izuwa ga wata halitta ko cibiya a cikin kwakwalwa mai suna” hypothalamus”. Wannan cibiya ita ce mai daidaita ɗumin jikina da naki da naka; idan dumin yayi kasa sai ta kara; idan kuma yayi yawa sai ta rage.
Haka kuma, wasu lokutan musamman idan muka shaki iska mai ƙarfi lokacin sanyi, mukan ga hancinmu yana yoyyon majina; me ya sa? Jikin dan adam kullum cikin ƙoƙarin kare mutum yake daga cuta. Saboda haka a kokarin jiki na kare shigar cututtuka ta hanyar iskar da muke shaka, ya sa majina ke fita daga hancinmu.
Yadda abin yake shi ne: a cikin iska akwai da datti da ƙura, da cututtuka iri-iri. To da zarar mun shaki irin wannan iskar, kwayoyin halitta da ke ɗamfare a bututun iska da makogwaro za su gane cewa ka shaƙi gurbatacciyar iska. Nan da nan bututun iska, wanda ya fara daga kofofin hanci zuwa cikin huhu, sai ya fara samar da majina.
Amfanin majinar shi ne tarfa datti da ƙurar da ke cikin iska wadda zata iya lahani ga jikin ɗan adam. Idan akwai cutuka da yawa a cikin dattin da ke iska, to tabbas kwayoyin halittar da suka gina bututun iska za su samar da majina mai yawa, har ma ta fara fitowa ta hanci.
Saboda gudun kar mu yaɗa cuta, yana da kyau mu guji fyace majina a jikin bango dan kada wani ko wata su taba da hannunusu, sannan kuma suyi amfani da hannun wajen cin wani abu, ko yaɗa cuta ta hanyar musabiha da wani.
Yanzu kuma bari mu ga hanyoyin da ya kamata mu bi domin kula da kanmu lokacin sanyi.
- Mu dinga yawan shan ruwa, saboda hakan zai taimakawa jikinmu ta fuskoki da dama kamar karawa kwayoyin halittar jikinmu kuzarin ci gaba da gudanar da ayyukansa.
- Mu dinga motsa jiki saboda hakan zai sa tsokokin jikin mu su samar da zafi ko ɗumi domin amfanar jikinmu lokacin sanyi.
- Mu dinga kula da fatarmu don kada ta bushe lokacin sanyi. Kamar yadda kuka gani, fata tana taimakawa wajen samar da dumi a jikinmu. Wanka, ko da sau daya ne, da shafa mai a jikinmu kan taimaka wajen hana bushewar fata.