Zargin Ina nuna wariya ko na gaza yin aiki ba gaskiya ba ne – Minista Sadiya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Umar Farouk ta bayyana cewa ba gaskiya ba ne iqirarin da wasu ke yi cewa wai ba ta rarraba ayyuka a dukkan sassan Nijeriya, sai wani wuri kaɗai, sannan kuma wai ba ta yin aikin ta yadda ya kamata.

Ta ce ita ayyukanta tana gudanar da su ne a kowace jiha a ƙasar nan da kuma Gundumar Babban Birnin Tarayya.

Ministar ta yi wannan kalami ne a raddin da ta yi wa wani wai shi Bibi Dogo wanda ya saka talla a jaridar Daily Trust ta ranar Litinin, 9 ga Agusta, 2022 inda ya yi kira ga Shugaba Buhari da ya kore ta saboda wai ba ta yin aikin ta yadda ya kamata.

A sanarwar da mai taimaka wa ministar a fagen yaɗa labarai, Nneka Ikem Anibeze ta bayar, ta bayyana cewa a zahiri Dogo, wanda ya ce shi dattijo ne a Jam’iyyar PDP a Ƙaramar Hukumar Bauchi, ya yi magana ne a madadin wasu waɗanda ke adawa da ministar, waɗanda za a iya gane su ta hanyar ƙarairayin da su ke yaɗawa.

Ta ce iƙirarin da ya yi ba gaskiya ba ne ko kaɗan, kawai ya wawuko shaci-faɗi ne a kan ministar da ofishinta.

Misali, Dogo ya ce wai ministar tana amfani da dukiyar gwamnati ta na yin “katsalandan” a siyasar Jihar Bauchi, sannan wai tana yin haka ne domin mara wa siyasar mijinta baya a takarar zama gwamnan jihar da ya ke yi a ƙarƙashin tutar Jam’iyyar APC.

Haka kuma ya ce ministar ba ta yi komai ba wajen taimakon matan jiharta ta Zamfara.

A cewar Anibeze, manufar wannan mutum wanda bai ma san kakakin jam’iyyar su na yanzu ba, shi da masu ɗaukar nauyinsa, ita ce su yaudari mutane da labaran ƙanzon kurege tare da haifar da tsana da gaba, sannan su ɗauke hankalin ma’aikatar tare da shafa wa aikin ta kashin kaji.

Ta ce in ba domin kada wasu tsiraru su gaskata ƙarairayinsa ba, to da ma’aikatar ba ta ce masa ƙala ba, amma ya zama wajibi a amsa masa don gyara illar da ya ke son kawowa kuma a tabbatar wa da masu ruwa da tsaki da kuma miliyoyin mabuƙata masu amfana da ma’aikatar a faɗin ƙasar nan cewa zarginsa ba gaskiya ba ne.

Ta ce a Arewa maso Gabas akwai jimillar masu cin moriyar shirin N-Power su 167,412 kuma a cikin su mutum 31,942 ‘yan Bauchi ne, yayin da ‘yan makarantar firamare da ma’aikatar ke ciyarwa a yankin sun kai 1,603,617 waɗanda yara 444,099 daga Bauchi ne.

Na biyu, wannan dattijon ya yi ƙaryar wai mutanen yankin Kudu maso Gabas suna zargin ministar da nuna masu wariya, wai ba ta kai aikin tallafi a jihohinsu ba.

Akasin hakan, a cewar mataimakiyar, akwai ‘yan makarantar firamare 778,450 da ake ciyarwa, sannan a ƙarƙashin shirin N-Power akwai mutum 136,629 a yankin.

Na uku, ya yi iƙirarin wai sama da masu cin moriyar N-Power su 80,000 ba a biya su kuɗin su na watanni biyar ba.

Ta ce wannan ma ƙarya ce domin mutum 14,021 da ba a biya kuɗin wata biyar ba su ne su ka jawo, domin komfutar tsarin biyan alawus na Gwamnatin Tarayya da ake kira ‘Payment system Government Integrated Financial Management Information System’ (GIFMIS) ita ce ta dakatar da biyan su a watan Maris na 2020 saboda dalilai daban-daban.

Dalilan sun haɗa da: mallakar asusun banki sama da ɗaya, da yadda masu cin moriyar shirin su ke amfani da asusun wajen karɓar kuɗaɗe (na albashi ko alawus) daga hukimomi daban-daban na Gwamnatin Tarayya ko kuma su ma’aikatan dindindin ne ko sun shiga wasu shirye-shiryen na gwamnati.

Ta bada misali da Jihar Bauchi, inda tsarin GIFMIS ya warware matsalolin mutum 191 masu cin moriyar shirin har an biya su kuma sun fita daga shirin.

Su kuma ‘yan N-Power na rukunin ‘Batch C’ an kasa su gida biyu ne, wato C1 da C2. A cikin Satumba 2021 aka ɗauki ‘yan C1 kuma za su kammala shirin a wannan watan na Agusta 2022 bayan sun cika wa’adin watanni 12 a cikin shirin.

Ta ce babu wata ƙumbiya-ƙumbiya wajen biyan, kawai mutum ya yi amfani da tsarin da gwamnati ta amince da shi wajen biya, wato NASIMS, inda duk wani mai cin moriyar shirin zai iya ganin dalilin da ya sa aka biya shi ko aka ƙi biyan shi, misali saboda qin zama ya yi aiki.

Su kuma ‘yan rukunin C2 da aka zaba, sun gama tirenin da tantancewar gani da ido ta hanyar abokan aikin ma’aikatar na hukumar NYSC. An fara tura mutum 490,000 aiki a ranar 1 ga Agusta inda za su fara shiga gurbin masu cin moriyar N-Power mutum miliyan ɗaya da Shugaban Ƙasa ya amince a ɗauka.

A ƙarshe, ta tabbatar wa da jama’a da abokan hulɗa cewa wannan ma’aikatar ta na nan ba gudu ba ja da baya wajen sauke nauyin da aka ɗora mata.

Ta ce ta lura da yadda ake ɗaukar nauyin wasu domin su kai wa ma’aikatar da ministar hari a kafafen yaɗa labarai don a vata masu suna, amma wannan duk yarfen siyasa ne maras amfani.

Saboda haka ba za ta tsorata ba ko a ɗauke mata hankali daga kan turbar da ta ke a kai ta kai wa mabuƙata agajin da su ke buƙata.