‘Yan bindiga sun kashe lauya a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kashe lauya mazaunin Zamfara, Barista Benedict T. Azza Esq. sannan suka yar da gawarsa a gefen Babbar Hanyar da ke kusa da ofishin FRSC, Gusau.

Shugaban ƙungiyar lauyoyin Nijeriya (NBA) reshen Gusau, Barista Junaidu Abubakar Esq. ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka miƙa wa Blueprint ranar Jumma’a.

Barista Abubakar ya ce, “A jiya da misalin ƙarfe 2230 na safe a gidana na samu kiran waya har sau uku daga abokan aikinmu inda suka sanar da ni cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba ne suka harbe B.T. Azza Esq, kuma gawarsa na kwance a bakin titin Byepass kusa da ofishin FRSC. Gusau.

“Bayan samun labarin, sai na garzaya wurin inda na gamu da abokan aikinmu, Abdullahi Ibrahim Esq. da Ibrahim Sani Gusau Esq tare da jami’an tsaro da yawa (’yan sanda da sojoji), na ga gawar BT Azza kwance cikin jinni a gefen hanya. Na kuma ga motarsa ​(Lexus Jeep) a gefen hanya.

“Muna can ne jami’an hukumar FRSC suka zo wurin ɗauke da jakar sanya gawa suka ɗauke shi sannan ‘yan sanda suka kai gawar zuwa Asibitin ƙwararru na Yariman Bakura da ke Gusau inda aka ajiye ta.”

A cewarsa, bayanan da ya samu sun nuna cewa, Barr. Benedict Wasu ‘yan bindiga 2 da ba a san ko su waye ba da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suka zo kan babur ne suka harbe shi har lahira.

Ya ƙara da cewa, “Bayanan sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun so yin garkuwa da shi ne a gidansa da ke Unguwar Saminaka, dake bayan hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC), hedkwatar Byepass, Gusau, amma ya samu nasarar tserewa, ya tuƙa motarsa ​​da gudu zuwa kan hanya amma ‘yan bindigar suka bi shi suka harbe shi har lahira.”

Maƙwabci marigayin wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce, sun ji ƙarar harbe-harben bindiga a yankin, bayan wani lokaci kuma sai suka ji ƙarar haɗarin mota.

“Lokacin da suka fito suka garzaya wurin da lamarin ya faru, sai suka ga Marigayi Barr Benedict ya buɗe ƙofar motarsa, ya fito yana tafiya da kafafuwa zuwa babban titin inda ya zauna sai ya fara zubar jini kuma ya mutu nan take.”

Blueprint Manhaja ta tattaro cewa marigayin wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka harbe shi har sau uku, inda bayan harbe-harben suka cika rigarsu da iska a lokacin da suka ga mutane na zuwa wurin.

Rahoton ya gano cewa, Marigayi Barr Benedict. T. Azza shi ne shugaban ƙungiyar Benedict Torngee Aza & Associates, Legal Practitioners, Gusau, jihar Zamfara.

Barr. Benedict Azza ya fito daga Yelewatta, Makurdi jihar Benue. Ya yi aratu a GCSS, Udei a 1999 da Jami’ar Jos da Nigerian Law School, Kano Campus a 2008, ya auri Izuagie Rachael har da ‘ya’ya.