2023: APC za ta ci zaɓe duk da matsalar tsaro a Nijeriya – Adamu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya, Sanata ya ce suna da yaƙinin samun nasara a babban zaɓen 2023 duk da tarin ƙalubalen da ƙasar ke ciki musamman matsalar tsaro da matsin rayuwa.

Sanata Abdullahi Adamu ya shaida wa BBC cewa irin waɗannan matsalolin, musamman na tsaro, ba kawai a Nijeriya ake fuskantar su ba har ma da wasu ƙasashen a duniya.

Ya bayyana cewa: “Ba shakka akwai taɓarɓarewar tattalin arziki a ƙasa, amma mai hankali ya san cewa taɓarɓarewar darajar naira ba wai mu muka haddasata a nan ba, batun tsaro kuma babu wata ƙasa da za ka ce tana zaman lafiya.”

Sai dai ya ce duk da haka gwamnati na iya ƙoƙarinta na ganin an magance matsalolin.

Nijeriya dai ta shafe tsawon shekaru tana fama da ƙaruwar matsalolin tsaro a sassan ƙasar.

A cewarsa, Jam’iyyar APC na aiki ne domin samun nasara a zaɓen da ke tafe sai dai ya ce akwai mutanen da ba ‘yan jam’iyyarsu ba da suke musu zagon ƙasa kan wannan ƙudirin nasu.

Sanata Abdullahi Adamu ya ce batun haɗa ‘yan takarar shugaban ƙasa da mataimaki duka Musulmai abu ne da yake ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce sai dai ya ce suna fatan ƙara ƙaimi wajen janyo ra’ayin ‘yan ƙasar ga amincewa da wannan zaɓi.

Ya ce zai yi wuya a iya shawo kan al’ummar ƙasar kan wannan haɗi saboda “an samu wani hali ne a ƙasar da ko me ka ce, akwai waɗanda suka lashi takobin ba za su yarda ba kuma ba yadda ka iya da su” amma tun da ana kan tsarin dimukuraɗiyya ne, kowa yana da ikon ya riƙe ra’ayinsa.