Nasarar Atiku nasarar Nijeriya ce – Lamiɗon Adamawa

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya kasance a gida yayin da ya kai ziyarar girmamawa ga mai Martaba Lamiɗon Adamawa Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha.

Ziyarar mai cike da tarihi ta samu halartar manyan mutane daga sassan ƙasar nan, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Namadi Sambo, Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa Sanata Iyorchia Ayu da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP Ifeanyi Okowa da tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu da tsohon gwamnan Adamawa Boni Haruna sai kuma sarakunan Mubi da Ganye da sauran masarautun jihar ta Adamawa da sauran abokan Atiku Abubakar.

A jawabinsa, Atiku Abubakar wanda ke riƙe da sarautar Wazirin Adamawa, Mukami na biyu Mafi girma a masarautar, ya bayyana matuƙar jin daɗi saboda kasancewarsa a gida domin sake dunƙulewa da mutanensa.

Ya bayyana godiyarsa ga Lamiɗon na Adamawa saboda gagarumar tarbar da aka yi masa a ziyarar mai cike da tarihi wadda ita ce ta farko tun da ya zama ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023.

Ya ce irin goyon baya da bunƙasa da harkokin siyasarsa ke yi, ya samu ne saboda addu’o’in masarautar.

Ya kuma yi alqawarin kasancewa jakadan masarautar nagari da jihar da yankin da kuma dukkan Nijeriya, inda ya ce tarihi ya nuna shi wajen irin rawar da ya taka don samar da shugabanci nagari.

Daga ƙarshe ya yi addu’ar samun haɗin kai da ɗorewar zaman lafiya tsakanin dukkan ƙabilun ƙasar nan.

A nasa ɓangaren, Lamiɗon Adamawa ya yi wa Atiku Abubakar maraba da zuwa, tare da tawagarsa, inda ya ce kasancewar Atiku Abubakar ɗan takarar shugabancin Nijeriya na PDP yana da matuƙar muhimmanci, saboda haka nasararsa a zaɓen fitar da gwani za ta zamo nasara babba ga Nijeriya a yayin da ƙasar ke faɗi-tashin ganin ta tsaya akan taswirar ci gaba.

Ya ce masarautar tasa da jama’ar Adamawa suna alfahari da shi saboda nasarorin da ya cimma wajen haɗa kan ƙasa wanda ko yaushe burinsa shi ne zaman lafiya da haɗin kai da ci gaban ƙasa, inda ya ce jarin da Atiku ya sanya wajen gina ɗan Adam abin alfahari ne.

Lamiɗon Adamawa ya ce yana da yaqini kan ƙwarewar Atiku wajen ɗaukar nauyin shugabanci a duk lokacin da aka ɗora masa.