Zawiyyoyi da gudunmawar su wajen ilmantarwa da inganta rayuwar al’umma

Daga Tahir Lawan Muaz Attijaneey

Gabatarwa:

Da sunan Allah, mai rahama mai jinƙai, tsaira da amincin Allah su tabbata ga Shugaban Talikai Sayyadina Rasulillahi ɗan Abdullahi da Aminatu, tare da Ahlin gidansa tsarkaka da Sahabbansa baki ɗaya.

Bayan haka, wannan maudu’i da aka ba ni na yi bayani a kansa ƙarƙashin wannan mu’asasah ta AL-SUFF FOUNDATION yana da matukar faɗi, hasali ma idan muka ɗauke shi gaɓa gaɓa za muga ya ƙunshi ɓangarori biyu manya wato bayani kan zawiya sai kuma gudunmawarsu wajen ilmantarwa da inganta rayuwa.

Har ila yau, idan muka koma za mu ga cewa shin ana so ne a yi bayani a kan tarihin hakan ko kuma ana so ne a kalli yadda ya kamata zawiyoyi su zama a wannan zamani na ƙarni na 21? Duk waɗannan da ma wasu abubuwa na sanya abun ya zamo da faɗi, amma saboda rashin lokaci mai tsawo da kuma kasancewata ba na iya yawaita rubutun ‘typing’ na ga na taƙaita abin na bi shi da ‘audios’ da za su ƙarfafi gaɓoɓin da zan tattauna su.
Saboda haka na raba bayanina izuwa nukɗoɗi kamar haka:

1. Ma’anar zawiya
2. Taƙaitaccen bayanin kan tarihin zawiya a Musulinci
3. Gudunmawar da zawiyoyin ɗarikun sufaye suka bayar na:
a. Ilmantarwa
b. Jihadi
c. Kyautata tsarin zamantakewa
4. Zawiyoyi a yau ina mafita?
5. Cikawa.

  1. Ma’anar zawiya a lugga da isɗilahi:

Kalmar Zawiya a harshen Larabci an samo ta ne daga tushen  (ز و ى)  jam’inta shi ne zawiyat da zawaya, ma’anarta ita ce gefe nako loko na wani bigire, daga wannan ma’ana aka samo suna zawiya na isɗilahi ta yadda mutane suka zamo suna ware loko a cikin gidajensu don su riƙa sallah ko karatun Alkur’ani da wirdai.

An rawaito ɗaya daga makarantar Alƙur’ani da ake kira Abubakr bn Iyyashin da aka fi sani da SHU’UBAH ɗaya ne daga marawaita Alƙur’ani daga makaranta 7, almajirin Asimu, lokacin da zai rasu sai ‘yar’uwarsa ta fashe da kuka sai ya kalle ta ya ce meye ya sa za ki yi kuka? Ki duba waccan zawiyar (ya yi nuni da lokon da yake karanta Alƙur’ani ) ɗan’uwanki ya yi saukar Alƙur’ani dubu 18 a cikinta.

Daga haka sai ma’anar ta koma tsakanin sufaye da suka zamo suna keɓewa don bauta a wani wuri musamman masallatai da ba na juma’a ba suke kiransa ZAWIYA, shi ya sa sai ya zamo lafazin ya shahara a hannunsu, har ila yau sufayen nan sun zamo masu sadaukantar da kansu ne wajen koyar da al’umma addininsu da kuma aiki da ilmin a zahiri da baɗini, sannan idan jihadi ya tashi za su miƙe su amsa kira daga zawiyoyi, wannan ma’anar ta ƙarshe ta sanya aka sansu a wasu ƙasashe da sunan MARABIT ko Ribat, musamman a ƙasar Misra, amma galibi irin waɗannan an fi gina su a gefen daular Musulinci don zaman kare iyakoki, kamar yadda za mu ga a nan ƙasar Hausa Sheikh Muhammadu Bello ya zauna a Wurno don zaman ribaɗi, to sufaye kan yi amfani da waɗannan RIBAT a matsayin wajen bauta da kare ƙasar Musulinci.

A wasu ƙasashen kuma ana kiran zawiyoyi da sunan KHANIQAH خانقاه musamman a ƙasashen Farisa wadda kalmar ma ta Kahanikah an samo ta ne daga Farisanci, su bambamcinsu da sauran shi ne asali an samar da su ne a hanyoyin sarakuna don zuwa yaƙi da ayyukan daula domin sarki ya tsaya da jama’a don hutawa da cin abinci daga ƙarshe suka zamo wurin ajiye mabuƙata da masu bauta zahidai. A wasu ƙasashen kuma ana kiransu TAKAYA ko TAKIYYAH التكية التكايا musamman a ƙasashen Turkiyya zamani daular Usmaniyya, wato Ottoman Empire.

A taƙaice, a iya cewa Zawiya a isɗilahi wuri ne da aka tanade shi domin zaman masu ibada da masu neman ilmi da mabuƙata da kuma ciyar da su da kula matafiya masu wucewa wato عابر سبيل da masu jihadi da shirya su domin kare daular Musulinci.

Da wannan bayani za mu gane cewa zawiya wata mu’assasah ce ta addini da ilmi da take jawo mutane ta hanyar wuridi da zikirai na ɗariƙun sufye wajen wanke musu zukata da taimaka musu da kuma amfani da su wajen kare Musulunci, sannan ba ta tsaya nan ba ta shiga cikin rayuwar al’umma da bada gudunmawa mabambata.

2. Taƙaitaccen bayanin kan tarihin Zawiya a Musulinci:

Yana da matuƙar wahala a iya cewa ga lokacin da Zawiyoyi suka fara a tarihin Musulinci saboda abu ne da ya ta’allaƙa da abubuwa da dama kamar jihadi da bayyanar sufaye da shehunansu, shi kuma sufanci ba ya yiwuwa sai da wajen bauta da zaman muridai, shi kuma sufanci ya zamo abu ne mai zaman kansa a Musulunci daga ƙarni na biyu.

Don haka ma iya cewa  a dunƙule tarihin zawiyoyi ya fara ne a Musulunci kamar yadda muka nunar tun farkon ƙarni na biyu a cikin gidaje amma zawiya da tsarinta a matsayin muasassah mai tsari tsayayye to ya yi jinkiri har wajejen ƙarni na huɗu zuwa na shida a ƙasashen Maghrib, wato Algeria da Tunisia da Morocco da sauransu. Duk da cewa dukkan ayyukan zawiya ana yin su tun ƙarni na biyu a ƙasashen Larabawa da Farisa da Masar wanda daga baya kuma tsarinsu ya yi ƙarfi a ƙasashen na Maghrib da muka yi bayani.

Tsarin zawiya ya zamo ya yi ƙarfi ne musamman sabida alaƙar Sharifai musamman a magrib da yadda suka zamo mafaka ta waɗanda ake muzguna wa a siyasance, har ta kai zawiyoyi suna shiga sha’anin siyasa su yi tasiri musamman a ƙarnonin baya-bayan nan, misali a kan haka shi ne zawiyar Sunusiya a Libya da Zawiyar Tijaniya ta Shehu Umarul Futy a ƙasashen Afrika ta Yamma musamman Mali da Senegal da maƙotansu, kamar yadda za mu gani, haka irin yadda aka kafa daular Idisiyya ta kakannin Shehu Tijani a Morocco ƙarƙashin tuta ta sufanci da sharifta.

3. Gudunmawar da zawiyoyin darikun sufaye suka bayar na:

Na ɗaya: Ilmantarwa:

Kamar yadda aka nuna a bya cewa Sufaye sun zamar da zawiya wajen karantarwarsu da koyarwarsu, wannan ya sanya dukkan zawiyoyi da aka sani a duniyar Muslunci suka zamo wurare ne na karantarwa da ɗaukar koyarwar Annabi (SAW) kasancewar sufaye masu kira zuwa ga gyaran zuciya sun zamo sun fi maida hankali wajen gyara halaye da koya adabu na nafsu da alaƙarta da mahalicci, hakan baya yiwuwa ba tare da sanin ilmin shariah ba kamar yadda Imamul Juniad yake cewa ‘ilminmu wannan abin daurewa ne da Alƙur’ani da Sunna wanda ya zamo ba shi da rabo cikinsu to ba ya tare da tafiyar mu.”

Wannan ya sa suka ɗora muridai kan neman ilmin Alƙur’ani da sunna har ya zamo manyan masana na Hadisai suka riƙa fita ta ƙarƙashin waɗannan zawiyoyi, kai har manyan waɗanda ake ce-ce-ku-ce a kansu cikin sufanci duniya ta shaida malamai ne, misali anan shi ne Babban Sufin nan Mansurul Hallaj, wanda ya yi karatu mai zurfi a wajen Junaid da Sahlu at Tusturi, da abul Hasani Annuri, shi kansa Sahlu Tustury melami ne na Sunna da aka cira masa hula a fagen ilmin Hadisi da tafsiri.

Haka akwai malamai irins Ibn Khafif Ash shirazi wanda Imam Az Zahabi yake cewa shehi ne abin koyi kuma babban masanin fiƙhu, mafi girma daga wannan shi ne Imamul Ghazali wanda ya rayu a matsayin maraya a hannun wani sufi da ya fara kula da tarbiyyarsu a zawiyarsa kuma mun san yadda ya zamo malami da duniya ba wai kawai ta Musulunci ba har ƙasashen yamma sun zamo suna cira masa hula a fagen sani a fannoni daban-daban.

Daga manyan zawiyoyi da suka bada gudunmawa ta ilmi akwai zawiyar Sayyidi Abdulwahab Ash-shaarani a cikin ƙarni na 10, wadda Alƙali Muhyiddin yai masa waƙafinta da kula da mazauna ciki tsawon rayuwarsu sarakuna da masu kuɗi suka riƙa ɓata kuɗi don tarbiya da koyar da addinin Allah, dubban muridai suka riƙa kwarara suna kwasar ilmi na sufanci da shari’a.

Hakan ya ba su damar yin karatu mai zurfi da fidda masana, sun zamo suna kwana karatun Alƙur’ani da koyar da shi da har mai littafin Tabakat ash shafi\iyyah yake cewa mutane suna jin gunji kai kace gunjin ƙudan zuma saboda karatu a cikin ta dare da rana.
Bayan wannan ga majalisu na ilmi da aka tsara, da zarar mai koyar da ilmul Hadith ya tashi mai tafsir zai zauna yana tashi mai sufanci zai zauna.

Zawiyar shehu Tijani rta a Fas ma ta ciri tuta wajen bada ilmi ya ishe mu ishara yadda shehu yake zama ana jefo masa mas’aloli masu zurfi na ilmi yana warwarewa.

Haka idan muka zo nan za mu ga yadda zawiyar Shehu Ibrahim ta zamo cibiyar ilmi daidai da zamani haka kuma zawiyoyin Shehu Atiku da sheu Tijani Usman da shehu Mai hula suka zamo, waɗanda suma an fitar da su ne a kasan zawiyoyin Sheikh Malam Abubakar Mijinyawa da Shehu Malam Muhammadu Salga. Waɗannan zawiyoyi su ne suka zamo fitalar ƙasar Hausa a ƙarni na 9 zuwa na 20.

Na biyu: Jihadi

Daga gudunmawar zawiyoyi a duniyar Musulunci akwai jihadi, wanda shi kuma yana kasancewa wajen yaɗa Musulunci ko kuma kau da zalinci daga kan waɗanda ake zalinta ko kuma nema wa ƙasashen yanci, a duk waɗannan ɓangarori Zawiyoyi sun bada gudunmawa mai girman gaske, za mu ɗauki kowanne ɓangare mu gani.