Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Fitina tun tana ’yar ƙarama a kan kashe ta don in an yi sake sai ka ga ta na girma a kullum har a wayi gari ta gallabi kowa. Kowa zai amince da cewa ita fitina ta kan shafi har wanda bai san hawa ba bare sauka. Mun ga yadda fitinar Boko Haram ta fara daga majalisa a waje ɗaya da sunan karatu ta hanyar nuna kin jini ga ilimin boko hara lamarin ya kai ga harba albarusai da manyan bindigogi. Ga shi dai tun 2009 a ke ta fama kwantar da wannan wuta amma har yanzu da sauran rina a kaba. A garin kashe wutar ma har kuskure a kan samu a taɓa rayuwar waɗanda ba abokan gaba ba.
Mun tuna lokacin da jirgin sojan ƙasa ya sauke bom kan taron jama’a a Rann da ke iyakar Nijeriya da Kamaru da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutum 50 da su ka haɗa da ’yan gudun hijira. Za ka ga yara ƙanana da su ka zama marayun da ba ’yan uwa kusa bare nesa don ta yiwu duk fitinar ta yi sanadiyyar rasa ransu. Ga arewa maso yamma da arewa ta tsakiya inda tun arangamar manoma da makiyaya a ka koma kan ɓarayin shanu har fitinar ta bunƙasa kai hare-hare da gamawa da ƙauyuka. Yanzu ga shi an shiga ƙalubalen satar mutane da ambata miliyoyin Naira a matsayin kuɗin fansa.
An yi ta samun zargin wasu jami’ai na rashin adalci wajen hukunci idan an samu laifin da za a iya biyan diyyar da ba ta taka kara ta karya ba, sai ka ga an tashi da garken shanu. Abin baqin ciki wasu daga matasa masu kiwon shanu sun juye daga riqe sanda sun koma riqe ƙatuwar bindiga ƙirar AK 47. Mu fa a shekarun baya ko labarin ’yan fashi a ka samu ba a tunanin za a samu ’yan arewacin Nijeriya da hannu a ciki. Ba a ma batun satar mutane don wannan baƙon abu ne ainun a wajen mutanen yankin Arewa mai jihohi 19. Shi ya sa in an kama wanda a ke tuhuma da satar mutane sai ka ji ko sunan satar ma bai iya faɗa da harshen Turanci.
Da zarar mutum ya shirya tafiya musamman mai bin titunan arewacin Nijeriya ba ma irin a yankin Arewa maso yamma da jihar Neja sai balbalinsa ya tashi. Mutum na ganin na gabansa ya rage wuta ko ya tsaya kama ruwa sai ya firgita ya zaci can gaba ba lafiya. Ko kuma mutum ya yi minti 5 zuwa 10 ya na tafiya a dokar daji bai gamu da wata mota ta gilma ba to lalle akwai tashin hankali. Babban makami shi ne addu’a da dogara ga Allah wanda shi ne ubangijin sammai da ƙassai masanin gaibu mai ba da kariya ba da biyan awalaja ba. Wannan yankin Arewa kenan da masu fitinar sun haɗa da masu neman kuɗi ta hanyar kisan gilla da kuma masu yaɗa aƙidar da ba ta kan hanyar gaskiya.
Can Kudu maso Gabas kuma batun masu son su bantare kansu daga Nijeriya ne don kafa ƙasar Biyafara. Wannan tsohon zance da ya kai ga gwabza yaqin basasa a Nijeriya. Madugun ’yan awaren marigayi Odumegwu Ojukwu ya fito ƙarara da alfahari ya nuna ya ji daɗin yadda ya jagoranci yaƙin yunƙurin kafa Biyafara amma ba buƙatar sake yin irin wannan yaƙi. Haƙiƙa Ojukwu ya ga yadda shi kan sa sai da ya arce Ghana kain shugaba marigayi Shehu Shagari ya yi ma sa ahuwa ya dawo Nijeriya.
Yaqin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubbai da ma gigicewar da yaqin ya haddasa yunwa ta gama da mutum miliyan 2. Dakarun sojan gwamnatin Nijeriya sun fara kama birnin Fatakwal ne inda waɗanda Ojukwu ya yaudara su ka yi ta ja da baya da tunanin wasu masu zuga su daga ketare za su kawo mu su ɗauki har lamarin ya zama duk fata ta dusashe.
Mata da yara sun galabaita, wasu sun mutu mazaje sun kwanta sai kuka da nadama da zama a sansanonin gudun hijira. Ɗaya daga sojoji a ɓangaren ‘yan Biyafara Christopher Ejike Ago ya ce, don qarancin abinci ya kai ga sojojin Biyafara na cafke ɓeraye su na ci. Ago ya ce bayan yaƙi ya wargaje mu su ya yi ƙoƙari ya samu ’yar shinkafa ya garzaya don neman iyalin sa inda ya yi sa’a ya same su, su ka yi ta murna musamman don sun ɗauka ya mutu sannan kuma ga shi ya samo shinkafa!
Tsohon sojan ya ce, gabanin fara yaƙi, Ojukwu wanda shi ne gwamnan soja na jihar gabashin Nijeriya kan zo da jirgi mai saukar angulu harabar jami’ar Nijeriya Nsukka inda ya ke bayanai na jan hankalin ɗalibai su rungumi aƙidar kafa Biayafara a matsayin shi ne samun ’yancin ƙabilar Ibo. Ya ce, duk lokacin da Ojukwu ya zo to karatu a jami’a ya ƙare sai a gamu a wani dandali da ke makarantar a yi ta shan bayanai.
Ago ya ƙara da cewa, da a ce Ojukwu ya bi shawarar mutanen sa da kuma tafiyar da abin sannu a hankali, da sun ci nasarar da ta fi abin da su ka taɓuka har aka wargaza shirin su. Ago ya ce, an kashe abokan sa a wajen yaƙi. An yi amannar cewa, mutanen da su ka mutu a sanadiyyar yunwa sun fi waɗanda bindiga ta kashe. Na ga bayanan da ke nuna soja sun kashe mutum dubu 45 ne amma yunwa ta kashe mutum miliyan biyu. In haka me ye ribar irin wannan yaƙi kuma me ya sa mutane kan jefa kan su a rijiyar da ba su da gugar da za a jawo su a fito da su waje in cikin rami ba lafiya? Bayyanar Nnamdi Kanu da ya kafa ƙungiyar dawo da Biyafara ta IPOB babban koma baya ne ga ƙabilar Ibo.
Dalilin koma bayan kuma hakan ya zo ne shekaru da dama bayan Ibo sun murmure daga yaƙin da su ka jefa kan su a ciki bayan ’yan uwansu, sun yi kisan gilla ga Sir Ahmadu Bello Sardauna, Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa, Ladoke Akintola da sauran su. Ba ma wannan kaɗai ba, Ibo sun warware kafa sun kafa kasuwancin su a duk lungunan Nijeriya musamman yaƙin Arewa mai faɗin gaske da damar ciniki da cin riba. Kanu wanda bai yi la’akari da hakan ba, ya hure wa sauran matasa kunne inda har ya kafa wata muguwar ƙungiyar ’yan ta’adda mai taken ESN da ke amfani da makamai wajen kashe jami’an tsaron Nijeriya da ma ’yan Arewa da kan gudanar da harkokin kasuwancin a yankin na su.
Dattawan Arewa sun yi hanzari su ka hana kowa maida martani kan kisan da ’yan IPOB ke yi wa ’yan Arewa don ƙiyayya kawai. Su kan kashe su kona su yanke kai su hura wuta su na rawa da iya shege a wajajen tsafin su.
Duk lokacin da ka ga mutane sun ɗauki makamai su na kisan gilla ba bisa ƙa’idar shari’a ba to ka tabbatar wataran za su juyo su shige kashe kan su da jama’arsu ko ma masu yi mu su tafi su na shewa da jinjina. Bayan kashe marigayi tsohon mai ba wa shugaba Jonathan kan siyasa Barista Ahmed Gulak, shaiɗanun ’yan awaren sun shiga kashe wasu manyan mutane a yankin su da ba mamaki ko sun lura ba sa mara baya ga muguwar hanyar da su ka ɗauka.
Kwanaki ma a lokacin da su ka kafa dokar hana fita a ranakun Litinin, wasu yara mata za su tafi makaranta, su ka tare su, su ka kwaɓe su tsirara su ka ci zarafin su duk da sunan kafa ƙasar Biyafara. ’Yan kasuwar shanu na arewa na cikin sabuwar kasuwar su a Aba jihar Abia, miyagun su ka shigo haka kawai su ka kashe su. Har yau babu abin da aka yi ko da kuwa a ce bin kaɗu da turo tawaga don ba da diyya ko ta’aziyya ta kwarai ga ’yan uwan marigayan da akasarin su mutan Gombe ne.
Kammalawa;
Rundunar sojan Nijeriya ta yi tir da ƙungiyar ’yan awaren Biyafara ta IPOB don kashewa da fille kan sojoji biyu a jihar Imo. Miyagun irin sun tare soja mai suna Linus Audu da wacce ya ke shirin su yi aure da ita Gloria Matthew wacce ita ma soja ce, su ka kashe su da kuma fille kawunan su. Gloria dai ’yan jihar Imo ce daga qaramar hukumar Nkwerre wacce ke tafiya gida da Linus don gabatar da shi ga iyaye a ɗaura mu su auren gargajiya. Kakakin rundunar sojan Onyema Nwachukwu ya ce, ’yan ta’addan da ke tutiyar kare al’ummar kudu maso gabas ba su duba ’yar yankin su Gloria ba, su ka kashe ta da wanda ta ke ƙauna.
Nwachukwu ya ce, wannan na nuna ’yan IPOB ba muradun Ibo su ka ƙarewa ba, ’yan ta’adda ne kawai.
Rundunar ta yi matuƙar nuna baqin cikinta kan kisan gilla ga jami’an nata guda biyu. Haƙiƙa kashe waɗannan sojoji na nuna yadda hatta kawance da ɗan Arewa a wajen ’yan awaren babban laifi ne da hukuncinsa kisa ne. Ta kan yiwu Gloria ta samu miji ɗan Arewa kuma ta jagorance shi zuwa Kudu da hakan ya kamata ya ja ma sa mutunci don ya na ƙaunar ’yar ƙabilar Ibo. Aƙalla dai miyagun za su iya samun uzuri daga masu sharhin adalci son in sun bar wa Gloria masoyin ta da jan kunnen sa ya guji shiga yankin su ba na miyagu ba sallama. Kazalika in da sun ji tausayin Gloria sun kyale ta da ran ta da ba su kaucewa muradun IPOB na kashe bare da barin ’yan gida ba.
