Tarnaƙin da Saraki zai iya fuskanta a neman shugabancin Nijeriya duk cancantarsa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

A kwanakin baya ne tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya bi sahun wasu jiga-jigan ‘yan siyasar Nijeriya, inda ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar Shugaban Ƙasa a zaɓen 2023 da ke gabatowa. 

Wakilin Blueprint Manhaja, John D. Wada, ya gudanar da bincike da kuma nazari na musamman, inda ya gano wasu qalubale waɗanda daga dukkan alamu za su iya zame wa tsohon Shugaban Majalisar Dattawan ƙafar ungulu a fafatawar ko da ya cancanta, kamar haka:

Saraki wanda tsohon gwamnan jihar Kwara ne na shekaru takwas ya sanar a shafinsa na yanar gizo cewa zai fito takarar shugabancin ƙasar nan a inuwar jam’iyyar PDP. 

Ya rubuta cewa, “a yayin da muke shirye-shiryen tafiyar nan, na tabbata dukkanmu za mu haɗa hannu don samun tikitin jam’iyyar mu mai adalci (PDP), inda za mu kuma gina ƙasa don amfanar kowa. Ku haɗa kai da ni don samar da ingantaccen tsaro da ayyukan yi wa iyalanku. Ba shakka sanin kowa ne cewa na ƙware sosai wajen ɗaukar ƙwararan matakai da suka dace.”

Bukola Saraki dai shine na biyu cikin tsofaffin shugabanin majalisar dattawa waɗanda kawo yanzu suka bayyana aniyarsu na fitowa takarar shugabancin Nijeriya. Na farko shi ne Anyim Pius Anyim wanda ya fara sanar da aniyarsa a inuwar jam’iyyar PDP shi ma. 

Tsohon Gwamnan Jihar Kwaran zai fafata ne a zaɓen fidda gwanin jam’iyyar PDP da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar da gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamnan Anambara, Peter Obi da dai sauran ‘yan takarar waɗanda su ka bayyana sha’awarsu na shugabancin ƙasar nan a PDP.

Kafin ma ya sanar da niyyar takarar na sa, ƙungiyar yaƙin neman zaven sa wato Saraki’s National Campaign Council a turance a ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Farfesa Hagher Lorwuese ta yi ta ziyartar yankunan ƙasar nan daban-daban inda ta sanar tare da neman albarka da shawarwarin wasu jigajigai waɗanda ake damawa da su a harkokin siyasar ƙasar nan don tabbatar da nasarar ɗan takarar (Saraki).

Ɗaya daga cikin wannan ziyara shine wanda suka kai wa Cif Edwin Clark da tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida wanda ya kwatanta Saraki da bindiga dake aiki da kansa wato Self Propelled Gun a turance. Ibrahim Babangida ya cigaba da bayyana cewa “ba shakka kun zaƙulo wanda ya dace da shugabancin ƙasar nan, muna buƙatar shugaba da zai yi amfani da bambance-bambancen mu wajen haɗa kanmu baki ɗaya.

Muna amfani da bambance-bambance dake tsakanin mu a ƙasar nan ta yadda bai dace ba. Na tabbata wannan matashin (Saraki) zai iya maido da martabarmu a ƙasan nan. Ba shakka Ina taya shi addu’a Ina kuma ba shi goyon baya,” inji Babangida.

Kodayake, a yayin da ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Saraki na cigaba da neman goyon bayan al’umma binciken wakilinmu ya gano cewa akwai wasu muhimman batutuwa da ka iya kasancewa ƙafar ungulu ko ƙalubale ga yaƙin neman zaɓensa a matsayin shugaban ƙasa.

Batun shiyya:
Ba shakka batun raba muhimman muƙamai ga shiyyoyin babban batu ne mai muhimmanci a siyasar Nijeriya. Duk da cewa doka ba ta tanadar da haka ba amma ana kallonsa a matsayin yarjejeniya na musamman ne don kowane ɓangare a ƙasa ya ɗanɗana mulki ya san ana yi da shi. 

Saboda haka a yanzu da aka bai wa shiyyar Arewa muƙamin shugaban jam’iyyar PDP, ana sa ran Kudu ne kuma za su fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar kamar dai yadda aka saba yi a jam’iyyar tun shekarar 1999. Ba shakka Saraki dake Arewa ta tsakiya a ƙasar nan ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar babban gangamin jam’iyyar PDP na shekarar 2021 da ya gabata.

A matsayin sa na shugaban kwamitin sasantawa na PDP ya zaga lungu-lungu da saƙo-saƙon ƙasar nan yana haɗa kawunan ‘ya’yan jam’iyyar dake ƙorafi ko rigima da juna kafin babban gangamin. Amma duk da haka ba dole ne tsarin rabon muƙaman ya yi masa yadda yake so ba. Duk da ba a riga an bayyana shiyyar da zai fidda ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023 ko ba. 

Amma a halin yanzu shugabannin siyasa da sauran masu ruwa da tsaki daga Kudu suna ta iƙirarin cewa shiyyar ne ya kamata ta fito da magajin Shugaba Muhammadu Buhari. Kimanin gwamnoni daga Kudu su 17 da wasu ƙungiyoyin siyasa daban-daban ciki har da ta Afenifere da Ohanaize da Pan-Nigeria da Delta Forum da sauransu ne suka nace dole mulki ya koma yankin su a shekarar 2023. 

A ‘yan kwanakin baya ma idan za a iya tunawa wani sanannen shugaba daga shiyyar wato Cif Edwin Clark ya yi kira ga masu sha’awar neman kujerar shugaban ƙasa daga Arewa su sauya tunanin su don haɗin kan ƙasa. 

Ya ce idan za a bi dokokin jam’iyyar PDP da kuma yarjejeniya da aka cimma a lokacin gangamin to yanzu lokaci ne na shiyyar Kudu ta fito da Shugaban Nijeriya a 2023 bayan Shugaba Buhari ya kammala wa’adin sa na shekaru 8. 

“Idan aka kuma samu akasin haka tamkar ana gayyatar tashintashina ne wanda ka iya haifar da rarrabuwar ƙasar mu,” in ji shi. 

Amma a nasa ɓangaren wani dattijon ƙasa, Alhaji Tanko Yakasai da yake mai da martani ga Cif Edwin Clark ya gargaɗe shi ya daina furta kalaman barazana a duk lokacin da yake tsokaci a batuttuwa da suka shafi ƙasa. 

Yakasai mai kimanin shekaru 90 a duniya ya ce duk da cewa shi ma yana cikin Waɗanda suka amince a bai wa Kudu damar, amma ya kamata su bi a hankali ne ba su riqa furta kalaman barazana ba. Sai dai duk da haka Saraki bai razana da batun shiyyar ba. Ya tava bayyana cewa duk da shiyyar Arewa ne ya fito da shugaban jam’iyyarsa PDP na ƙasa amma hakan bai hana duk ɗan takara daga kowace shiyya a ƙasar nan ya fito takara ba. 

Ya ce, “game da batun shiyya, jam’iyyar mu ta riga ta bayyana ƙarara a duka tarurrukan mu cewa kodayake mun riga mun raba muƙamanmu ga shiyyoyi musamman na jam’iyya, amma ba ta hana duk ɗan ta dake da niyyar fitowa takarar shugaban ƙasa ya yi haka ba. Abin da muke nema shine ɗan takara da ya dace mai farin jini wanda zai iya lashe zaɓen,” in ji shi.

Tuhume-tuhumen kotu:
Kamar yadda aka sani akwai wasu zarge-zarge da hukunce-hukuncen kotu da dama da suka mamaye wa’adin Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar dattawa. Idan za a iya tunawa akwai kuma shari’ar cin hanci da rashawa da aka zargi Saraki a lokacin da yake riƙe da muƙamin daraktan tsohon babban bankin al’umma na Nijeriya wato Society General Bank Nigeria (SGBN) da kuma lokacin sa a matsayin gwamnan jihar Kwara. 

An fara gurfanar da shi a gaban kotu ne jim kaɗan bayan zaɓen sa a matsayin shugaban majalisar dattawa maimakon ɗan takaran kujerar wanda jam’iyyarsa ta APC a lokacin ta fi so. Hakan ya ɓata wa shugabancin APC rai. 

Tun bayan rantsar da shi a watan Yunin shekarar 2015, shugabancin Saraki na majalisar ya mamaye da rigingimu daban-daban har ƙarshen wa’adinsa. An zarge shi da laifin haɗa baki da wasu jiga-jigan gwamnatin tarayya wajen danne wasu dokokin majalisar dattawar ta yadda aka fito da shi a matsayin shugaba. 

Rundunar ‘yan sanda ne suka gudanar da bincike akan batun wanda a ƙarshe aka gurfanar da shi Saraki da wasu muƙarrabansa a majalisar da suka haɗa da mataimakinsa Eke Ekweremadu da tsohon akawun majalisar Efeturi da wani tsohon akawun kuma wato Salisu Maikasuwa waɗanda duk aka zarge su da laifin a gaban Babbar Kotun Tarraya dake Abuja. 

Kodayake dukkansu sun musanta zargin, a shekarar ta 2015 hukumar kula da dukiyoyi wato Code of Conduct Bureau (CCB) ta zargi daraktocin babban bankin al’umma na Nijeriya a wata takardar qara da ta shigar ɗauke da zarge-zarge har guda 13, ciki har da rashin bayyana asalin dukiyarsa da Saraki ya ƙi yi. 

Saraki ya kuma ƙalubalanci sari’ar har zuwa Kotun Ƙoli, inda a shekarar 2018 Kotun Ƙolin ta wanke shi daga duka zarge-zargen. 

Har ila yau ita ma hukumar EFCC a shekarar 2021 ta tabbatar cewa ta gayyato Sanata Bukola Saraki don ya amsa wasu tamboyoyi da suka shafi karkatar da maƙudan kuɗaɗe da cin hanci da rashawa da sauransu. 

Daga bisani sai Saraki ya shigar da ƙara a wata Babban Kotu a Abuja yana ƙalubalantar zarge-zargen hukumar EFCC ɗin da kuma damar da hukumar ta samu na tuhumarsa a shari’ar da a cewarsa Kotun Ƙoli ta riga ta yi wats da shi. EFCC ta kuma buqaci a ƙwace wani katafaren gidan Saraki dake Legas wadda ta ce an sayo ne da zunzurutun kuɗi Naira biliyan ɗaya da miliyan 9 wadda ta ce aka sato daga asusun gwamnatin jihar Kwara. Amma daga bisani Babbar Kotu dake Legas ƙarƙashin mai shari’a Mohammed Liman ya yi watsi da ƙarar a watar Maris na shekarar ta 2021.

Ƙabilarsa a Arewa:
Masana harkokin siyasa sun ce ko da jam’iyyar PDP ta bar wa kowa daga kowace shiyya damar neman shugabancin ƙasar nan a inuwarta zai yi wuya Saraki ya shawo kan ‘yan Arewa su zaɓe shi, idan aka yi la’akari da rashin yawan ƙabilarsa a Arewa. 

Idan dai aka yi la’akari da doka da tanade-tanaden siyasar Nijeriya na shekarar 1999 da aka yi wa gyaran fuska, ba shakka Saraki ya cancanci fitowa neman takarar kujerar shugabancin Nijeriya. Sai dai ya fito ne daga Kwara, wato jihar da ke tsakiyar Arewacin ƙasar da ta daɗe tana fama da batun rashin yawan ƙabila ko ƙabilarsa ta Yarabawa a siyasance, wacce ta ke ba ta da yawa a Arewa, sai dai a Kudu. 

Saboda haka a taƙaice dai waɗannan da wasu dalilai da dama ne binciken wakilinmu ya gano za su iya jawo wa Sanata Bukola Saraki cikas a yaƙin neman kujerar shugaban ƙasar nan da yake yi.