Daga WAKILINMU
Gwamnan Jihar Barno, Babagana Umara Zulum, ya bada umarnin dakatar da cibiyar ACTED ta ƙasa da ƙasa mai zaman kanta bayan da aka gano cibiyar na gudanar da harkar horar da wasu mutane yadda ake harbin bindiga a cikin wani otel da ke Maiduguri.
Mai magana da yawun gwaman, Malam Isa Gusau, shi ne ya bayyana umarnin da Zulum ya bayar, tare da cewa cibiyar wadda ta ƙasar Faransa ce, an same ta tana amfani da bindigogin roba wajen bada horo kan yadda ake harbi da bindiga a wani otel a Maiduguri.
Gusau ya ce, mazauna yankin sun kai wa jami’ai rahoton cewa suna jin ƙarar bindiga na tashi daga otel ɗin lamarin da ya sa aka kai batun ofishin ‘yan sanda da ke GRA mai hurumin kula da yankin da otel ɗin yake.
Haka nan, ya ce binciken ‘yan sanda ya gano wasu ƙananan bindigogin roba a otel ɗin, yayin da biyu daga cikin waɗanda ake horarwar suna hannun ‘yan sanda don taimaka musu wajen bincikensu.
Sanarwar ta nuna ya zuwa lokacin da ‘yan sanda za su kammala bincikensu, Gwamna Zulum ya bada umarnin rufe otel ɗin da ma harkokin ACTED a faɗin jihar Barno.