Matawalle: PDP ta rasa APC ta samu

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan sha’anin kafofin sadarwa na zamani, Bashir Ahmad ne ya yi nuni da hakan a shafinsa na Facebook a Lahadin da ta gabata.

Inda ya wallafa cewa, “Ashe Zamfara ta dawo gida! Barka da zuwa Matawalle.”

Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari, Matawalle bai fito ya tabbatar da sauyin sheƙar nasa a hukumance ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *