Zuwa ga iyaye kan lalacewar ’ya’ya mata a wannan zamani

Spread the love

 

Jama’a, Assalamu Alaikum, barkanmu da wannan lokaci.

A cikin wasiƙata ta yau zan zayyana wasu abubuwa guda uku da ke kawo sanadiyyar lalacewar tarbiyyar ’ya’yanmu, musamman ma ’yan mata a wannan zamani.

Idan ka ji ko ki ka ji kina aikata ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa, kina ko kana amfani da ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa, sai ka yi ƙoƙari ka gyara ta hanyar rabuwa da wannan munanan abubuwa.

Domin yin hakan shi zai sa ka tsira ko ki tsira daga fazawa halaka, idan kuma ’yarka ko ɗanka yana ko tana amfani da irin waɗannan abubuwa to a yi ƙoƙari a gujesu tun kafin tura ta kai bango.

Bari mu kawo muku wazannan abubuwa kai tsaye domin taimaka muku da yi muku tuni akan cewar waɗannan abubuwa su ne suka zamo sanadiyyar lalacewar tarbiyyar ’ya’yanmu a yau.

Abu na farko shi ne;

1. Talla:

Talla tana da matuƙar haɗari da tasiri musamman ma talla irin wadda ’yan mata su ke yi wadda su ke fita kasuwa tallan Goro, Fiya Wata, Ƙuli da dai sauran kayayyakin da su ke talla, har ma gara tallan da ’yan mata su ke yi a gida ta kayan koli, wannan talla da su ke yi maganar gaskiya ba tallan kayan da ke kansu su ke yi ba, a’a, tallan kansu su ke yi saboda da zarar kin fara wannan talla ne za ki fara tara samari, wani ma saboda wata niyya da ke zuciyarsa zai sa ya sayi kayan da ki ke tallan, bawai don yana buƙata ba. kaga kuwa lalle wannan harka akwai haɗari, inda daga nan za ki tara samari ana wai ‘ke mai farin jini ce’, to maganar gaskiya idan saurayi ya zo miki da zancen soyayya ke da kanki za ki bayyana masa cewar ya fito, idan da gaske ya ke kin ga tun a wannan lokaci zai san kina da tunani, kuma kema a wannan lokaci za ki san da irin manufar da ya zo wurinki. Sannan ka da ki yarda ki biyewa daɗin bakinsa, domin idan har ya san Allah ne mai yi to ya bari sai ya shirya sai ya zo, ba yazo ya yi ta ɓata miki lokaci shekara ɗaya zuwa biyu a ji shiru bai fito ba, wannan shawara ce gare ku ’yan mata.

2. Iyaye mata baku da wani yaƙi a wannan zamani irin ku yi ƙoƙari ku hana ’ya’yanku mallakar wayar salula ta ‘Android’ domin mallakar wayar ga ’yan mata a wannan zamani tana da matuƙar haɗari wurin lalata musu tarbiyya, domin da ita ne samari su ke amfani su tada wa yara hankali su kuma cata musu rayuwa.

To kun ga kuwa amfani da wayar Android ga ’yan mata yana da haɗari domin ana iya turawa da bidiyo ta Whatsapp, Instagram, Tiktok, da Facebook, za a iya tura wa mutum ko wane irin bidiyo. A halin yanzu, da a bai wa mutum ’ya mace ace ka kula da tarbiyanta, gara a ba shi tunkiya guda goma a ce ya kula da su, domin ita tunkiya idan ka ɗaureta ko kamata shinge ba ta isa ta haura wannan shingen ba, amma ita mace sai ka ba ta tarbiyya na tsawon shekara goma, dare ɗaya ka nemi wannan tarbiyya ka rasa.

3. Irin ƙawayen da ’ya’yanku su ke mu’amula da su:

Yana da kyau ko wace uwa ko uba ya san irin ƙawaye, samarin ko mutanen da ’yarsu ko ɗansu ya ke ko ta ke mu’amula da su, domin ’yarka za ta iya kasancewa mai tarbiyya tsawon shekaru ashirin, amma rana ɗaya ka nemi wannan tarbiyya ka rasa saboda haɗuwa da ta yi da a

kawayen banza ko samarin banza wanda suka zamo sanadiyyar lalacewar tarbiyyarta. Kaga kuwa yana da kyau a riƙa ƙoƙari ana kula da hakan, domin tarbiyyarsu Allah ya bamu, idan ka kasa kula da tarbiyyansu, hakan zai iya zamema hanyar shiga wuta ko faɗawa cikin masifa da fushin Allah.

Saboda haka a shawarce a yi ƙoƙari matuƙa, sai fa an dage sosai wajen ba da tarbiyya, domin kullum tarbiyya daɗa lalacewa ta ke saboda yadda zamani ya ke daɗa gabatowa, ƙarshen duniya ya ke daɗa kusantowa sai muce Allah ya bamu damar kula da ’ya’yanmu da kuma basu tarbiyya mai kyau, Ilahy Ajib.

Daga Sayyid Alkazeem M. Shareef Alhasan. 08062740226.

By ukarofi