Ɗangote ya ki amince wa kamfanin NNPC ya ƙara hannun jari a matatarsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Rukunin Kamfanonin Ɗangote, Aliko Ɗangote ya ce kamfaninsa ya yi watsi da buƙatar da Babban Kamfanin Fetur a Ƙasa NNPC ya gabatar ta neman ƙara adadin hannun jarinsa a Matatar Ɗangote da kaso 7.25 cikin 100.

Ɗangote ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da shugaban asusun zuba jari na Norway, Nicolai Tangen, kamar yadda ra rahotanni suka bayyana.

An ruwaito cewa an samu ƙaruwar man da ake tacewa a matatar mai ta Lekki a Jihar Legas zuwa lita biliyan 3.18 a watanni uku na farkon 2026 yayin da man da ake shigowa da shi ya ragu sosai da lita miliyan 965.52.

Binciken da aka ƙara yi ya nuna cewa yaƙin Amurka da Iran da ya janyo matsalar mai ya haifar da ƙaruwar kuɗin shiga ga matatar Dangote yayin da matatar ta ƙara yawan tataccen man da take fitarwa.

A cewar Dangote, an ƙi amincewa da tayin NNPC na ƙara kashi 7.25 na hannun jarinsa a matatar saboda kamfanin yana shirin bai wa sauran ƴan Najeriya damar zuba hannun jarinsu a kamfanin.

By Babaji