Ƙasar Sin ce babban misali na yadda ya kamata demokraɗiyya ta kasance

Daga FA’IZA MUSTAPHA

Demokraɗiyya ita ce tsarin shugabanci dake mayar da hankali kan muradun al’umma.

Wato dai, al’umma ne ya kamata su kasance kashin bayan demokraɗiyya.

Kuma ƙasar Sin ce babban misali na yadda ya kamata demokraɗiyya ta kasance, domin a ganina, tabbatuwar tsarin demokraɗiyya ita ce, kasancewar al’umma cikin walwala da wadata da kwanciyar hankali.

Yayin da yake ƙaddamar da babban taron wakilan Jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20 a Lahadin da ya gabata, shugaban ƙasar Xi Jinping, ya jaddada cewa ƙasar za ta ƙara inganta tsarin demokraɗiyya dake mayar da hankali kan jama’a, wato jama’a ne za su kasance masu ruwa da tsaki a dukkan tsarukan demokraɗiyya a dukkan matakai.

Abun da na fahimta shi ne, a ko da yaushe, JKS ta kan tsara manufofi da dabarun da za su tabbatar da cewa, al’umma ne ke kan gaba a duk wani abun da ya shafi ƙasar, wanda ke nuna yadda take mayar da hankali wajen lalubo dabarun da suka dace da yanayin da take ciki domin amfanawa al’ummarta.

Ƙarƙashin shugabancin JKS cikin shekaru 100 da suka gabata, kowa zai iya shaida cewa, ƙasar Sin ta samu manyan nasarori na ban mamaki da babu wata ƙasa da ta samu a duniya.

Misali na baya-bayan nan shi ne, fatattakar talauci baki ɗaya.

Duk da yawan al’ummarta da kuma kasancewarta ƙasa mai tasowa, Sin ta yi abun da manyan ƙasashe suka gaza.

Ta tabbatar da dukkan al’umominta daga ƙabilu daban daban na cikin wadata ba tare da barin kowa a baya.

Haka kuma, ta tabbatar da cewa ana rayuwa cikin kwanciyar hankali da lumana a tsakaninsu.

Jama’a su suka san matsalolinsu, kuma damawa da su cikin harkokin ƙasa, shi zai kai ga ci gaban da ake muradi.

Wakilan jam’iyyar daga dukkan ɓangarori, da suka hada da manoma da ma’aikata daga ɓangarori daban-daban na samun damar wakiltar al’ummominsu yayin taron wakilan Jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar, lamarin dake kara jaddada cewa, al’umma ne ke jan ragamar demokraɗiyyar ƙasar, kuma wannan tsari ne ya kai ta ga samun ɗimbin nasarori.