Dabarar da Ƙasar Sin ta ɗauka wajen zamanintar da al’umma

Daga CMG HAUSA

A ranar Lahadin da ta gabata, aka ƙaddamar da babban taron wakilan Jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin (JKS) karo na 20 a birnin Beijing na ƙasar, inda Xi Jinping, babban sakataren jam’iyyar, ya gabatar da wani rahoto.

Cikin rahotonsa, Xi ya jaddada cewa, dabarar zamanintar da al’umma da ƙasar Sin da ɗauka, ana aiwatar da ita ne ƙarƙashin jagorancin JKS, tare da bin tsarin siyasa na Gurguzu.

Wasu halayen musamman da dabarar ke da su, sun haɗa da yadda ake ɗora muhimmanci kan moriyar jama’a, da ƙoƙarin samun daidaito tsakanin ɗan Adam da muhalli, gami da neman ƙulla hulɗar haɗin kai da ke iya amfanar dukkan ɓangarori masu ruwa da tsaki.

Ban da haka, dabarar zamanintar da al’ummar Sin ta ƙunshi wasu ginshikai, da suka haɗa da nacewa ga zama ƙarƙashin jagorancin JKS, da tsarin Gurguzu mai halin musamman na ƙasar Sin, da neman samun ci gaba mai inganci, da aiwatar da dukkan ayyukan gwamnati bisa tafarkin demokuraɗiyya, da baiwa dukkan al’ummar ƙasar damar samun wadata tare, da kafa al’ummar ɗan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai ɗaya a duniya, da ƙirƙiro sabon nau’in wayewar kai ta bil Adama, da dai sauransu.

Wannan bayanin da aka gabatar ya nuna hanyoyin da za a bi don raya ƙasar Sin zuwa wata ƙasar zamani mai bin tsarin Gurguzu.

Mai fassara: Bello Wang)