Matawalle ya ba da haƙuri kan rufe kafofin yaɗa labarai

Daga WAKILINMU

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ba da hakuri tare neman afuwa kan matakin rufe wasu kafafen yada labarai a jihar.

Kafofin yada labaran da lamarin ya shafa sun hada da tashar NTA da gidan Pride FM da ke Gusau, baki dayansu mallakar mallakin Gwamnatin Tarayya.

Sauran su ne tashar Gamji TV da Gamji FM da Al-umma TV wadanda suke masu zaman kansu.

Sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Ibrahim Dosara, ya fitar, ta nuna kafofin da aka rufen sun saɓa wa dokar jihar da ma ta aikin jarida, shi ya sa aka ɗauki matakin rufe su.

A ranar Litinin aka ga jigo a gwamnatin jihar, Dokta Abdullahi Shinkafi, ya miƙa wa tashoshin da lamarin ya shafa takardar ban-hakuri a madadin gwamnati, a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a Gusau.

Dokar da gwamnatin ta ce an take, ita ce wadda ta haramta tarurrukan siyasa a jihar saboda dalilai na tsaro.

Sai dai akwai zargin cewa gwamnati ta rufe kafofin ne saboda yada taron PDP da suka yi.