Mu ne tushen masana’antar Kannywwod – Sani Muazu

Daga AISHA ASAS

Ɗaya daga cikin tushe da asalin harkar finafinai a arewacin Nijeriya, Sani Muazu, ne shafin namu na Nishaɗi ya zaƙulo mu ku a wannan sati. A cikin tattaunawar, mai karatu zai ji asali da tushe na finafinan Hausa da kuma irin rawar da ya taka wurin kafuwar masana’antun finafinai musamman masana’antar Kannywwod. A sha karatu lafiya:

BLUEPRINT MANHAJA: Mu fara da jin tarihin rayuwarka.

SANI MUAZU: Sunana Sani Muazu, mai shirya finafinai. Na kwashe tsayin shekaru 30 a harkar. An haife ni a garin Jos, kuma a nan na taso, wato a nan na yi karatun firamare da kuma sakandare.

Na fara gabatar da shirye-shirye a gidan talbijin tun a ƙarni na 80, jim kaɗan bayan kammala karatuna na sakandare. Ina ɗaya daga cikin ma’aikata na farko-farko a gidan talbijin na PRTV Jos, a shekara ta 1982 kenan.

Baya ga haka, na tafi makarantar koyon aikin jarida da ke Iko, wato ‘Nigeria Institute of Journalism’, Lagos, inda na karanta aikin jarida, tun daga gabatar da labarai zuwa rubutawa. Daga ƙarshe na koma Jami’ar Jos a shekara ta 1989/1990, na yi digiri kan aikin na jarida. Daga nan na ɗora da kwasa-kwasai da dama na ɓangarori daban-daban.

Yaushe ka tsinci kanka a masana’antar finafinai ta Kannywood?

Ba shigowa masana’antar Kannywwod na yi ba, Ina cikin tushe da asalin masana’antar, ma’ana Ina daga cikin waɗanda suka kafa ta. Kafin Kannywwod, Ina cikin harkokin da suka jivinci talbijin wanda ya ƙunshe har ita kanta wasan kwaikwayo. A matsayina na mai gabatar da shirin talabijin, na kan yi amfani da damar wurin gabatar da labarai na finafinan nishaɗantarwa waɗanda su ne suka ƙyanƙyashe Kannywood. Idan ka yi duba da tarihi da jimawar fim ɗin ‘Turmin Danya’.

Ni da wasu abokan aikina ne mu ka fara shirya fim mai dogon zango wanda mu ka sanya wa suna ‘Bakandamiya’. Ni ne na rubuta, kuma na zama jarumi mai jan ragamar shirin, kuma Ina bada gudunmawa ta ɓangaren shiryawa. Shiri ne da aka yi ƙarƙashin inuwar gidan talabijin na NTA Jos.

A shekara ta 1990, ni da marigayi Matt Dadzie, wanda ya kasance abokin aikina, amma yana sama da ni, mu ka yi shawarar kafa kamfanin fim mai zaman kansa. To, mun yi nasarar yin hakan, mu ka sanya masa suna ‘Epitome Productions’. Finafinan Turanci masu dogon zango da gajeru da dama sun fita ta ƙarƙashin wannan kamfani namu, kamar, ‘Riddles’, ‘Hopes’, ‘Change’ da sauran su. Kuma wannan kamfani ya kafu ne a garin Jos.

A shekara ta 1993/1994 na yanke shawarar barin Epitome don buɗe na wa kamfanin na Karen kaina. Na jawo wasu daga cikin abokai mu ka ƙirƙire kamfanin ‘Lenscope Media’ wanda aka yi wa rijista a shekara ta 1995. Wannan duk fa ya faru ne kafin kafa Kannywood har ma da masana’antar finafinai ta Kudu, wato Nollywood. Kuma har yau Ina jan ragamar wannan kamfani, shakaru 27 kenan.

Kasancewar masana’antar fim na da ɓangarori da dama. A wane ɓangare ne ka fi shahara?

Na samu ƙwarewa a ɓangaren da ya shafi tsara finafinai tun daga yanayin hoto tsari da wurare, amma jimawa Ina aiki da daraktoci da dama ya bani damar ƙwarewa a ɓangaren. Kuma duk da cewa na fi son zama a bayan kamara, wato a ɓangaren shiryawa, na fahimci Ina da baiwar iya aktin, wannan ne ya sa tun da na ɗan fara, aka dinga nema na don fitowa a finafinai.

Ka taka rawa a shiri mai dogon zango na ‘Kwana Casa’in’, inda ka fito a matsayin gwanman Alfawa. Shin ya ka samu wannan matsayin?

A matsayina na jarumi, na samu gayyata ne daga gidan talabijin na Arewa 24, don gwaji na wannan rol na gwanman Alfawa a ‘Kwana Casa’in’, kuma na je. To, Ina ganin na yi abin da suke buƙata ne shi ya sa suka zave ni.

Ko akwai wani ɓangare ko wata rawa da ka taka da ke ba ka dariya a shirin?

Matsayin da na taka matsayi ne da yake son jarumta, don haka na yi iya ƙoƙari wurin bayyana izza da matsayi irin na gwamnan daidai yadda ake buƙata, har wasu ke ganin abin kamar da gaske. Tabbas akwai wurare da dama da suke na ban dariya, kamar lokacin da aka tuhumi gwamna a wani taro, duk da cewa na bayyanar da zafi irin wanda wannan layin ke buƙata, hakan bai hana shi zama abin dariya ga masu kallo ba.

Ko za mu iya sanin fim na farko da ka bada umurni?

Na fara bada umurni tun a ƙarni na 80, inda na faro a gidan talabijin kamar yadda na faɗa a baya. Na bada umurni a finafinai na talabijin da dama tun kafin zuwan Kannywood. Fim mai dogon zango na ƙarshe da na bada umurni shine ‘Buka Africana” wanda a yanzu haka ake haska shi a tashar Arewa 24.

Kawo yanzu, finafinai nawa ka shirya?

Ɗaruruwa. Gaskiya lissafin ma ya kuvuce min.

Wane irin cigaba ka samu a wannan tafiya?

Cigaban da na samu suna da yawa. Daga ciki akwai tava rayuwar matasa da yawa, waɗanda ta sanadiyyar abin da na fara suka yi sha’awa har ta kai sun shigo wannan harka ta finafinai, kuma sun zama wani abu a cikin ta.

Baya ga haka, mun koyar kuma mun bada aiki ga ɗaruruwan mutane da a yanzu su ma sun ɗauki wasu kuma sun koyar da wasu da dama.

A matsayina na shugaba a Kannywood, domin na yi zama shugaban ƙungiyar MOPPAN na ƙasa, wanda hakan ya ba ni damar zama jigo a wannan masana’antar, na yi nasarar shirya horo ko bita kan harkar fim ba adadi tare da taimakon ‘French Embassy’, ‘British Council’,American Embassy’, USAID da wasu da dama daga gwamnati da kuma ƙungiyoyi masu zaman kansu.

Wannan kawai ya samar da cigaba ga masana’antar, domin da yawa daga cikin masu fim ta kowanne ɓangare sun samu horo na musamman kan sha’anin harkar fim.

Kana so ka ce kai halattaccen ɗan ƙungiyar MOPPAN ne kai?

Tabbas ni ɗan cikin ƙungiyar ne har koyaushe.

Menene burinka a masana’antar Kannywood?

Babban burina dai cigaban masana’antar, a samu ƙwarewa da ƙarfi a cikin ta. Ta zama cikin jerin masana’antun finafinai na Afirika mafi ɗaukaka da ƙwarewa. Mu ga kanmu a jerin masu amsar Oscar, ma’ana mu zama jerin waɗanda hankalin duniya ya karkato kansu.

Na san ba za ka rasa samun ‘yan ƙalubale da ka dinga yin tuntuɓe da su a wannan tafiya ba?

Ƙalubale dai abokin tafiyar rayuwa ne. ba abin da ke zuwa da sauƙi a wannan rayuwa da mu ke ciki. Wata rana ka yi nasara kan abin da ka sa gaba, wata rana kuma ka samu tsaiko ko faɗuwa. Wasu su so ka, wasu su bayyana ƙiyayya ko hassada gare ka, amma dukka mun karve su da hannu biyu, mun ci gaba da tafiya, kuma alhamdu lilla, har yanzu mu na kan ƙafafuwanmu.

Wacce shawara za ka bai wa abokanen aikinka na masana’antar Kannywood?

A riqe gaskiya, domin ita gaskiya ita ce jagowa ga kawacce irin nasara. Su riƙe gaskiya a aikinsu. Su sani, ita harkar fim sana’a ce, amma akwai buƙatar su rinjayar da sha’awar ci gaban harkar fiye da samun kuɗi, hakan zai sa su yi mata sadaukarwar da mu mu ka yi mata. Su cire hassada da ganin ƙyashi, kuma su rage dogon buri. Ta hakan ne kawai za su samu ci gaba da ci gaban masana’antar.

Daga garshe, wane saƙo kake da shi zuwa ga masoyanka?

Yanzu mu ka soma, kuma yanzu ne mu ka sha ɗamar fara gudun samar da abin da zai ƙara ƙayatar da su. Fatan mu, su ci gaba da ba mu haɗin kai tare da linka soyayyarsu gare mu. Na gode.