Takardun kuɗin da suka shaida yadda ƙasashen duniya suka ci gajiyar ci gaban Ƙasar Sin

Daga LUBABATU LEI

Jama’a, in kun yi la’akari da takardun kuɗi na ƙasa da ƙasa, za ku gano da cewa, hotunan da aka buga a takardun kuɗi na wasu ƙasashen Afirka, da ma sauran wasu ƙasashe masu tasowa, suna da alaƙa da ƙasar Sin.

Zanenmu na yau ya kuma nuna wasu abubuwan da aka buga a takardun kuɗi na ƙasashen Aljeriya, da Sudan, da Madagarscar da Malawi, wadanda suke da alaƙa da ƙasar Sin.

In mun ɗauki takardun kuɗi na Aljeriya ga misali, za mu ga cewa, an buga hoton babban masallacin ƙasar da aka sanyawa sunan Djamaa el Djazaïr, a takardun kuɗin kasar mai darajar Dinar 1000, masallacin da ma’aikatan ƙasar Sin suka shafe tsawon shekaru shida suna ginawa, bayan daidaita wahalhalu da dama da suka fuskanta.

An ƙaddamar da masallacin ne a shekarar 2017, wanda ke iya ɗaukar musulmi kimanin dubu 36 a lokaci guda, wanda kuma ya kasance babban masallaci mafi girma na farko a nahiyar Afirka, kuma na uku a duniya baki ɗaya.

Sai kuma a takardun kuɗin ƙasar masu darajar Dinar 500, inda aka buga hoton tauraron ɗan Adam na sadarwa na farko a kansa, tauraron da ya kasance irinsa na farko a ƙasar, wanda ƙasar Sin ta yi nazarinsa tare da harba shi a shekarar 2017, wanda ya taimaka wajen daidaita matsalolin sadarwa da suka shafi rediyo, da talabijin da yanar gizo, da samar da ilmi da sauransu a ƙasar.

Baya ga haka, a ƙasar Sudan, madatsar ruwa ta Upper Atbara da kamfanin ƙasar Sin ya ɗauki nauyin ginawa, ta taka muhimmiyar rawa wajen daidaita matsalolin samar da wutar lantarki, da ruwan sha, da kuma ban ruwa ga miliyoyin al’ummar ƙasar, wadda kuma ta samar da gudummawar bunƙasa tattalin arziki da zaman rayuwar al’umma na ƙasar.

Sai kuma a Madagarscar, fasahar inganta irin shinkafa da masanan ilmin noma na ƙasar Sin suka samar ta sa yawan shinkafar da aka samar a ƙasar ta karu da yawan gaske, matakin da ya daidaita matsalar abinci ga al’ummar ƙasar da ke yawan dogara ga shinkafa.

Domin bayyana godiyarsu, ƙasashen biyu sun buga hotunansu a takardun kuɗin su.

Haƙiƙa, irin waɗannan labarai ba sa lisaftuwa. Cikin shekaru 10 da suka wuce, bisa ga shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, an aiwatar da shirye-shiryen gina gadoji, da tashoshin jiragen ruwa, da hanyoyin mota, da layukan dogo, da tashoshin samar da wuta, da filayen wasa da dai sauransu da dama a ƙasashen Afirka da ma sauran ƙasashe masu tasowa, wadanda suka ba da babbar gudummawa ga bunƙasuwar ƙasashen, da ma rayuwar al’ummominsu. A yayin da ƙasar Sin ta samu gaggarumin ci gaban tattalin arziki da zaman al’umma, ta kuma yi ƙoƙarin raba nasarorinta ga sauran ƙasashen duniya, kasancewarta tana rungumar makomar dan Adam ta bai ɗaya.

Kwanan nan, an buɗe babban taron wakilan Jam’iyyar Kwaminis da ke kan karagar mulki a ƙasar Sin ko (JKS) karo na 20, kuma a rahoton da ya gabatar wajen taron, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar mista Xi Jinping ya yi nuni da cewa, ƙasar Sin za ta ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasashe masu tasowa bisa sahihanci da gaskiya, don kiyaye moriyarsu ta bai ɗaya.

A sa’i ɗaya, ƙasar ta kuma, yi kira ga ƙasashen duniya da su yayata manufar kishin zaman lafiya, da ci gaba, da adalci, da dimokuraɗiyya da ‘yanci, don al’ummomin ƙasashe daban daban su ƙara kishin juna, su kuma martaba mabambantan wayewar kan duniya, su ƙara yin mu’amala da juna ta fannin al’adu, ta yadda za su kawar da sabani da rikice-rikice da suke fuskanta.

Zaman duniya, cuɗe-ni-in-cu dae-ka ne. A ganin ƙasar Sin, da ci gaban duniya baki ɗaya za a tabbatar da ganin ci gabanta, kuma ci gaban ƙasar zai taimaka ga tabbatar da ƙarin ci gaban duniya.

Al’ummar ƙasar Sin na son hada hannu da takwarorinsu na duniya, don rungumar kyakkyawar makomar dyan Adam ta bai ɗaya.

Mai zane: Mustapha Bulama